Yan ta'adda
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bukaci a cigaba da addu'a a kan rashin tsaron Najeriya. Ya yi magana kan yakin Iran da Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa an harbe babban dan bindiga Mai Jakka da ya shahara da fitowa a TikTok yana zagin gwamnati da yi wa 'yan Najeriya barazana.
Wasu rahotanni da muke samu sun tabbatarda cewa yan bindiga karkashin jagorancin dan ta'adda, Babaro sun kwace ikon ƙaramar hukumar Kankara a Katsina.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban PDP na mazabar Lade da dansa da wani mutumi a kauyen Mari, jihar Kwara.
Bayan Bello Turji ya gwabza da jami'an tsaro, gwamnatin Zamfara ta ce artabun da aka yi da ‘yan ta'adda ya zama gagarumar nasara wurin kisan yaran dan bindigar.
Gwamnan jihar Kebbi ya sanar da cewa zai kafa dokar kisa kan masu taimakon 'yan bindiga da bayanan tsaro yayin da ya je Zuru bayan kashe mutane kusan 30.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekara 27 a Osisioma, Abia, sannan suka sace kanwarsa kafin bikin aurenta.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa akalla mutane 24 sun mutu bayan wata budurwa 'yar kunar bakin wake ta tarwatse a wajen cin abinci a Konduga, Jihar Borno.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da bindigogi sun farmaki wasu kauyuka a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka mutane tare da kona gidaje masu yawa.
Yan ta'adda
Samu kari