Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, duka Fasinjojin da Ya Ɗauko Sun Rasu a Faransa

Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, duka Fasinjojin da Ya Ɗauko Sun Rasu a Faransa

  • Wani jirgin sama da ke amfani d shi wajen daukar masu koyon tsalle daga sama ya gamu da hatsari mai muni a gabashin kasar Faransa yau Lahadi
  • Rahotanni daga yankin sun nuna cewa matukin jirgin da fasinjojin da ya dauko duka, ciki har da malamai da ɗalibai sun mutu nan take
  • Gwamnatin Faransa ta tabbatar da ministan harkokin cikin gida, Laurent Nunez ya nufi wurin da hatsarin ya faru domin ganin halin da ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

France - Wani jirgin sama na farar hula ya yi hatsari a gabashin ƙasar Faransa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matukin jirgin da dukkan fasinjoji 10 da ke cikinsa.

Mahukuntan yankin sun tabbatar da cewa mutane 11 ne suka mutu a hatsarin da ya faru a kusa da filin jirgin saman garin Tomblaine a yau Lahadi, 28 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane

Jirgin sama.
Jirgin sama dauke da fasinjoji yana tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa rahotannin da suka fito daga yankin sun bayyana cewa jirgin na ɗauke da wata tawaga ce da ta je koyon ydda ake yin tsalle daga sama.

Dalibai da malamai sun mutu

Mahukuntan yankin sun ce wadanda suka rasa rayukansu sun haɗa da matukin jirgi, dalibai biyar da malamai biyar masu koyar da tsalle daga sama.

Bayan faruwar hatsarin, rundunar 'yan sanda ta bukaci mazauna yankin da su guji kusantar filin jirgin domin bai wa jami'an ceto damar gudanar da aikinsu ba tare da tangarda ba.

Ministan Faransa ya nufi wurin hatsarin

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa ta tabbatar da cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Laurent Nunez, ya nufi wurin da hatsarin ya faru domin duba halin da ake ciki.

Wannan hatsari na zuwa ne kusan makonni biyu bayan wani jirgin sama ya yi hatsari a Amurka, inda mutane 12 suka mutu a kusa da filin jirgin Butler Memorial da ke Bates County a jihar Missouri, kudancin birnin Kansas.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama fasto da hannu a sace dalibai, malamai? Yan sanda sun magantu

Jami'an tsaro sun kai dauki

Rundunar Missouri Highway Patrol ta bayyana cewa jami'anta sun isa wurin domin taimaka wa 'yan sanda da hukumomin yankin wajen gudanar da bincike, kamar yadda NBC News ta ruwaito.

Ta ce:

"Jami'anmu suna taimakawa Rundunar 'Yan Sandan Butler da Ofishin Sheriff na Bates County kan hatsarin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar mutane a kusa da Butler Memorial Airport."
Macron.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yana jawabi a taron manema labarai a birnin Faris Hoto: Sean Gallup
Source: Getty Images

Rundunar ta kara da cewa:

"Rahotannin farko sun nuna cewa dukkan mutane 12 da ke cikin jirgin sun mutu."

Sajan Justin Ewing na rundunar Missouri Highway Patrol ya bayyana cewa ana amfani da jirgin wajen kai mutane koyon yadda ake yin tsalle daga sama (skydiving).

Jirgin sama ya yi hatsari a Sudan ta Kudu

A wani rahoton, kun ji cewa akalla mutum 14 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a kusa da birnin Juba na ƙasar Sudan ta Kudu.

Kara karanta wannan

Hankulan mutane sun tashi kan yadda aka tsinci gawar budurwa a ɗakin saurayinta

Hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar (SSCAA) ta tabbatar da cewa jirgin ya faɗi ne da nisan kilomita 20 daga kudu maso yammacin babban birnin ƙasar.

Sudan ta Kudu, wadda ita ce ƙasa mafi ƙanƙanta a duniya, tana fuskantar ƙalubale mai girma a fannin sufurin jiragen sama saboda rashin ingantaccen tsari da tsofaffin jirage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262