'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Natasha, An Yi wa Sanata Barna a Gida
- Wasu bata-gari sun bi dare wurin kai farmaki gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti Uduaghan da ke Obeiba-Ihima a jihar Kogi
- Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun kimanin su uku, dauke da bindigu da sauran makamai sun kai harin da 1:00 na dare
- Wannan na zuwa awanni kadan bayan tsohon gwamna, Yahaya Bello ya karyata ikirarin da Natasha ta yi na cewa ana neman rayuwarta
- Duk da jami'an tsaro ba su kama ko mutum daya daga cikin maharan ba, amma an bayyana cewa an kaddamar da bincike a kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi –Wasu bata-gari dauke da takubba da bindigu sun kai farmaki gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Matasan sun kai hari gidan da ke unguwar Obeiba-Ihima a karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi, a safiyar ranar Talata.

Asali: Facebook
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa Babban Jami’in Tsaron Sanata Natasha, Yakubu Ovanja, ne ya kai rahoton harin ga hukumomin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ovanja ya bayyana cewa harin ya auku da misalin karfe 1:00 na dare, inda akalla mutane uku dauke da makamai suka lalata ginin gidan, har da farfasa tagogi.
Jami’an tsaro sun kai dauki gidan su Natasha
Rahoton ya ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda ta Okehi sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru cikin gaggawa.
Babu wanda aka ji rauni ko aka kashe, kuma ba a samu kama ko daya ba, amma an dauki bayanai daga wurin domin fara bincike a mataki na farko.

Asali: Original
Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa ba a tabbatar da dalilin kai harin ba tukuna yayin da bincike ke ci gaba.
Sanata Akpoti-Uduaghan, wacce fitacciyar ‘yar siyasa ce a yankin Kogi ta Tsakiya, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.
Sanata Natasha ta yi zargin za a kashe ta
A baya-bayan nan, Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, na da hannu wajen kitsa wani yunkuri na kashe ta a karamar hukumar ta.
Yayin dawowarta gida domin ganawa da mutanenta, Natasha ta shaida musu cewa Akpabio ya hada baki da Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo, da tsohon gwamna Yahaya Bello, domin kashe ta.
Ta kara da cewa sun shirya dorawa al’ummar mazabarta laifin kisan nata, duba da yadda rikici ke kara dagulewa tsakaninta da shugaban majalisar dattawa.
Yahaya Bello ya musanta zargin Natasha
A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya shigar da kara gaban Sufeto Janar na ‘yan sanda bisa zargin Natasha Akpoti da bata masa suna.
A cikin wata wasika da lauyansa, N.A. Abubakar, ya fitar ranar Laraba, Bello ya bukaci rundunar ‘yan sanda ta Najeriya da ta gayyaci Natasha domin yi mata tambayoyi.
A baya, Natasha ta zargi Yahaya Bello da gwamnan Kogi mai ci, Ahmed Ododo, da karbar umarni daga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, domin hallaka ta a Kogi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng