Bulama Ya Tono yadda Boko Haram da 'Yan Bindiga ke Tara Kudin Sayen Makamai
- Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewa sayen makamai da kira ga mutane su kare kansu zai ƙara jawo tabarbarewar tsaro
- Ya bayyana cewa 'yan ta'adda kamar Boko Haram sun karɓi sama da Naira biliyan 1 a matsayin kudin fansa tun daga 2024
- Bukarti ya ce a yanzu haka wasu 'yan siyasar Borno ba su iya zuwa mazabunsu saboda suna karkashin Boko Haram
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Lauya mai sharhi kan al'amura, Audu Bulama Bukarti, ya bukaci magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya cikin tsari da bin doka.
Lauyan ya bayyana hanyoyin da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ke tara miliyoyin kudi da suke amfani da su wajen sayen makamai da sauransu.

Asali: Facebook
Ya fadi haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV, inda ya soki kiran tsohon Ministan Tsaro, Laftanar Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya), na cewa mutane su kare kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Bukarti, kira irin na TY Danjuma na iya haifar da ƙarin tashin hankali da ɓarkewar rigingimu, ganin yadda makamai ke yawo a hannun jama'a a Najeriya.
Yadda 'yan ta'addan Najeriya ke tara kudi
Bukarti ya bayyana cewa babbar hanyar samun kuɗi ga 'yan ta'adda musamman a Arewa maso Yamma da Boko Haram shi ne kudin fansa.
Ya ce Boko Haram sun kwace iko a wasu yankunan jihar Borno, suna da kasuwanni, kotuna, inda wasu 'yan siyasa ba zu iya zuwa mazabunsu saboda suna karkashin Boko Haram.
A cewarsa:
"Akwai rahotanni da ke nuna cewa Boko Haram sun karɓi sama da Naira biliyan 1 tun daga shekarar 2024."
Ya ƙara da cewa idan har aka bai wa waɗannan gungun 'yan ta'adda kasafin kuɗin Najeriya na shekara guda, za su iya lalata ƙasar baki ɗaya.
Bukarti ya kara da cewa suna daura haraji wa manoma, masu kiwon dabbobi da masu kama kifi domin samun kudi.
Ya bayyana cewa wani dan ta'adda ya taba cewa sayen biredi ya fi wahala a Najeriya a kan sayen bindiga.
Lauyan ya ce suna amfani da kudin wajen sayen makamai, babura da sauransu domin cigaba da ta'addanci.
TY Danjuma: Bukarti ya soki kira a kare kai
A yayin da yake mayar da martani ga kiran da aka yi wa 'yan Najeriya su kare kansu, Bukarti ya ce hakan ba mafita ba ce.
Ya ce:
"Yin hakan zai ƙara jawo yawaitar makamai a hannun jama'a. Za a samu ƙarin kashe-kashe,"
Ya ce kiran bai dace da matakin da Najeriya ke ciki ba, inda ya bukaci gwamnati da ta ƙara inganta tsarin tsaro da yin gaskiya wajen amfani da kuɗin tsaro.

Asali: Facebook
A karshe, Bukarti ya ce yana da muhimmanci a daina fakewa da kare kai don kaucewa kafa ƙungiyoyi masu zaman kansu da za su iya komawa barazana ga zaman lafiya.
Boko Haram sun fara bidiyo a TikTok
A wani rahoton, kun ji cewa Audu Bulama Bukarti ya ce a yanzu haka 'yan Boko Haram sun fara sakin bidiyo a TikTok.
Lauyan ya ce ko kwanan nan wani dan Boko Haram ya yi bidiyo yana masa barazana bayan ya yi magana kan tsaro.
Bukarti ya bukaci gwamnatin tarayya da ta hada kai da TikTok domin toshe shafukan 'yan ta'addan ko da ba za a iya binsu a kama su ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng