Abin da Gwamnatin Katsina Ta ce da Aka Kama Shugabannin Ƴan Ta'adda a Filin Jirgi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Gwamnatin Katsina ta ce ba za ta iya tabbatar wa ko musanta rahoton kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ba a filin jirgi
- Ministan Harkokin Cikin Gida ya ce an kama mutane bakwai da ake zargin kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne bayan dawowarsu daga Hajji
- Wasu majiyoyi sun ce ana zargin wadanda aka kama da alaka da ‘yan bindiga, yayin da DSS da NIS ba su tabbatar da lamarin ba har yanzu
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina – Gwamnatin jihar Katsina ta ce ba za ta iya yin tsokaci kan rahoton da ke cewa an kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan ta'adda ne a filin jirgin Umaru Musa Yar’Adua bayan dawowa daga aikin Hajji na 2026 ba.
Wannan na zuwa ne bayan ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar cewa an kama mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da kungiyar ISWAP ne a filin jirgin Katsina.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Source: Facebook
Katsina ta ce lamarin na hannun tarayya
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce batun yana karkashin ikon hukumomin tsaro na tarayya ne kawai a cewar rahoton Daily Trust.
Da yake magana da jaridar da kuma BBC Hausa, Danmusa ya ce gwamnatin jihar ba ta gudanar da wani kamu a filin jirgin ba kuma ba ta da ikon tabbatar da rahoton.
Ya ce:
“Wadannan batutuwa na tsaro da gudanarwa ne da hukumomin tarayya ke kula da su. Gwamnatin jihar ba ta da hurumin tabbatarwa ko musanta wannan rahoto.”
Ya bukaci masu neman karin bayani su tuntubi Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya DSS.
Kwamishinan yada labarai ya ce bai sani ba
A nasa bangaren, kwamishinan yada labarai da al’adu na Katsina, Bala Salisu Zango, ya ce bai samu labarin kama wani shugaban ‘yan bindiga da ya dawo daga Saudiyya ba.
Ya ce:
“Ban san wani batu na kama shugabannin ‘yan bindiga da suka dawo daga Saudiyya ba.”
Rahoton ya jawo cece-kuce a Katsina
Duk da bayanin gwamnatin jihar, lamarin ya ci gaba da haifar da muhawara, musamman bayan wasu zarge-zargen baya da ke cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun samu damar zuwa aikin Hajji ta hanyar shirin jihar.
Mai sharhi kan harkokin siyasa, Dr Bashir Kurfi, ya taba zargin cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun samu tallafin zuwa Hajji ta hannun gwamnatin Katsina.
Sai dai gwamnatin jihar ta sha musanta wannan zargi, kamar yadda rahoton Daily Post ya nuna.

Source: Original
Wata majiya ta yi karin bayani
Wata majiya daga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta ce an gudanar da kamen ne a filin jirgin Katsina, amma ta ce wadanda aka kama ba kwamandojin Boko Haram ko ISWAP ba ne.
Majiyar ta ce ana zargin wasu daga cikinsu shugabannin ‘yan bindiga ne, sannan wasu ‘yan kasar Nijar ma na cikin wadanda aka kama bayan dawowa ta filin jirgin.
Sojoji sun dura maboyar 'yan ta'adda
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun ci gaba da hana 'yan ta'adda sakat a jihar Katsina ta hanyar mai samame a maboyarsu cikin daji.
Sojojin sun sake kai wani harin bazata a maboyar 'yan ta'adda da ke karamar hukumar Matazu inda suka yi musayar wuta da hatsabibai.
A yayin artabun, sojojin sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda tare da raunata wasu daga cikinsu da kuma kwato makamai.
Asali: Legit.ng

