Sabuwar Kungiyar 'Yan Damfara Ta Bulla a Kebbi, Gwamnati Ta Bayyana Barnar da Suke Yi

Sabuwar Kungiyar 'Yan Damfara Ta Bulla a Kebbi, Gwamnati Ta Bayyana Barnar da Suke Yi

  • SaniGwamnatin jihar Kebji ta bayyana cewa ta shirya yakar mambobin kungiyar 'yan damfara ta yanar gizo da ke cutar mutane
  • Mambobin kungiyar dai na kai hari kan mutanen da suka kasance fitattu a cikin jama'a domin tatsar kudade masu kauri a hannunsu
  • Gwamnatin ta bayyana cewa mambobin kungiyar sun kware wajen yi wa mutane kutsa kuma suna yin barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana gagarumin yaƙi da wata sabuwar kungiyar masu aikata laifuffukan yanar gizo da aka sani da “Yan Vocal".

Gwamnatin ta yi alƙawarin tarwatsa hanyoyin sadarwar su da kuma gurfanar da waɗanda ke da alhakin karuwar damfara ta yanar gizo, tsoratarwa, da kuma karɓar kuɗaɗe ta hanyar barazana a hannun mutane a ciki da kuma wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu

Gwamnatin Kebbi za ta yaki 'yan vocal
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ya fitar ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026.

Su waye mambobin kungiyar 'Yan Vocal?

Gwamnatin ta ce ingantattun bayanan sirri sun nuna cewa kungiyar, wanda mafi yawancinsu matasa ne 'yan tsakanin shekaru 19 zuwa 24, suna gudanar da ayyukansu ne daga sassan karamar hukumar Argungu.

Matasan sun ƙware wajen kutse a shafukan sada zumunta, ƙirƙirar fuskokin ƙarya a yanar gizo, da kuma amfani da barazana da tsoratarwa domin karɓar kuɗaɗe a hannun mutane.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana ayyukan ƙungiyar a matsayin wata barazana ga al'umma da kuma tsaron ƙasa, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

“Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna tsananin damuwa kan ayyukan wata sabuwar ƙungiyar laifuffukan yanar gizo da aka fi sani da 'Yan Vocal' kuma ta sake jaddada kudirinta da wajen bada kariya ga jama'a daga dukkan nau'ikan laifuffukan yanar gizo."

Kara karanta wannan

Kotun Najeriya ta yanke wa Ibrahim da Abdullahi hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Ahmed Idris

Ya suke gudanar da ayyukansu?

A cewar gwamnatin, ana zargin mutanen da ake nema suna kai hari ga masu amfani da shafukan Facebook, WhatsApp, TikTok da sauran dandalolin sada zumunta ne ta hanyar tura musu hotuna ko bidiyoyi na batsa ko kuma sauya fasalin kiran bidiyo da hotuna kafin su tsoratar da mutanen da abun ya ritsa da su domin su biya su kuɗaɗe.

Sanarwar ta ƙara da cewa kungiyar yake nufar fitattun mutane, ciki har da masu riƙe da madafun iko na siyasa, shugabannin gargajiya da na addini, 'yan kasuwa da sauran shahararrun mutane a faɗin Najeriya, da kuma ƙasashe maƙwabta kamar su Nijar, Ghana, da kuma Jamhuriyar Benin.

'Yan damfara sun bulla a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta bayyana cewa binciken farko ya gano mutane 19 da ake zargi mambobin ƙungiyar ne, yayin da hukumomin tsaro suka gano hanyoyin gudanar da ayyukansu, wuraren tarurrukansu, da kuma hanyoyin da suke amfani da su wajen karɓar kuɗaɗen haram ta hanyar dandalolin hada-hadar kuɗi na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta shigo Arewacin Najeriya? 'Yan sanda sun gano gaskiya

Kungiyar 'yan ta'adda ta bulla a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta yi magana kan kan bullar wata ƙungiyar asiri mai alaƙa da ta'addanci mai suna ‘Sai Malam’.

Gwamnatin ta bayyana cewa kungiyar na gudanar da ayyukanta a yankin karamar hukumar Argungu da ke jihar.

Hakazalika, gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa tana tattaunawa da hukumomin tsaro domin shawo kan lamarin kafin ya kazanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com