Yobe: Mutane Sun Shiga Mawuyacin Hali da Ƴan Ta'adda Suka Tarwatsa Gada da Bam
- Ƴan ta'adda da ake zargin mayakan ISWAP ne sun kai faramaki kan wata gada a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi amfani da bam wajen ruguza gadar da ke hafa garuruwan Ngurbuwa da Goniri
- Wannan lamari dai ya jefa mazauna yankin cikin mummunan hali kuma ya hana zirga-zirga tsakanin garuruwan guda biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton mambobin ƙungiyar ISWAP ne, sun tarwatsa gadar da ke haɗa Ngurbuwa da Goniri a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Bayanan da aka tattaro sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun tarwatsa gadar ne ta hanyar amfani da tashin bam a harin da suka kai ranar Alhamis da ƙarfe 10:30 na dare.

Asali: Original
Ƙwararren masani kan tsaro da yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar Alhamis inda ‘yan ta’addan suka yi amfani da bam wajen lalata sauran sassan gadar da ke haɗa garuruwan biyu.
Ƴan ta'adda sun tashi bam a jihar Yobe
Rahotanni sun bayyana cewa wannan harin ya jefa mutanen yankin cikin halin kunci, inda yanzu haka ba su samun sauƙin wucewa daga wuri zuwa wuri.
Wani jami’in kungiyar sa-kai a garin Gujba wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar Leadership cewa harin ya auku ne da lokacin da ƴan ta'adan suka kutsa kauyen Goniri.
Haka zalika, wani dagacin ƙauyen da shi ma ya buƙaci a ɓoye sunansa saboda tsaro ya tabbatar da rugujewar tsohuwar gadar da ke haɗa Ngurbuwa da Goniri.
Wane hali mutanen yankin suka shiga?
Ya bayyana cewa mazauna yankin na shan wahala sosai wajen kokarin tsallaka wa daga gari zuwa gari sakamakon ruguza gadar da ‘yan ta’addan suka yi.
Wasu daga cikin mazauna Ngurbuwa sun roƙi gwamnatin jihar Yobe da ta ɗauki matakin gaggawa ta hanyar tura karin jami’an tsaro domin kare sauran gadoji da ke yankin.
Mallam Aliyu, wani mazaunin yankin, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta tura isassun jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumar Gujba domin kawo ƙarshen hare-haren ‘yan ta’adda da ake fama da su.

Asali: Twitter
Mutane ba su iya barci a kauyukan Yobe
Mutumin ya ce:
“Mazauna yankunan Gujba, Buni Yadi, Goniri da Katarko ba sa iya yin barci da ido biyu a daren kowace rana saboda fargabar hare-hare.”
Aliyu ya kara da cewa ‘yan ta’adda sun tilasta wa manoma da ‘yan kasuwa a yankin daina ayyukansu, musamman da rana saboda tsoron farmakin Boko Haram.
Boko Haram ta farmaki sojoji a Borno
A wani labarin, kun ji cewa ƴan Boko Haram sun sake kai kazamin hari a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
An ruwaito cewa ƴan ta'addan sun kutsa kai garin Yamtake da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka kashe sojoji da fararen hula.
Wata majiya ta ce kafin isowar dakarun da aka tura kai ɗauki, mayakan Boko Haram sun kutsa kai cikin sansanin soji da ke Yamtake.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng