Bulama Bukarti Ya Gargadi Gwamnati kan Mu'amalar Boko Haram da Mutane a TikTok

Bulama Bukarti Ya Gargadi Gwamnati kan Mu'amalar Boko Haram da Mutane a TikTok

  • Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana yadda ‘yan Boko Haram ke amfani da TikTok don yada ra’ayoyinsu da yin barazana ga jama’a
  • Ya ce ‘yan ta’addan na gudanar da shirye-shiryen kai tsaye da amsa tambayoyi lamarin da ke kara musu karbuwa da samun hadin gwiwa
  • Ya soki hukumomin tsaro da gwamnati bisa gazawarsu wajen hana ‘yan ta’addan amfani da kafar TikTok don yi barazana ga Bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shahararren lauya kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Audu Bulama Bukarti, ya ce ‘yan Boko Haram na yin amfani da kafar TikTok cikin sauki a Najeriya.

Audu Bulama Bukarti ya ce suna amfani da TikTok ne don yada ra’ayoyin ta’addanci da barazana ga jama’a.

Bukarti
Bulama Bukarti ya bukaci ya bukaci toshe asusun 'yan ta'adda a TikTok. Hoto: Audu Bulama Bukarti
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Bukarti ya ce sabon salon ya fara ne da barayin daji, amma yanzu har ‘yan Boko Haram na gudanar da shirye-shirye kai tsaye a TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Bukarti ya ce suna karanta sakonnin mutane, amsa tambayoyi da kuma yada ra’ayoyin da za su haddasa tashin hankali.

Bukarti ya ce wasu daga cikin bidiyon da ‘yan ta’addan ke wallafawa suna tara dubban masu kallo, kuma idan ba a dauki mataki ba, za su iya fara yada hare-hare kai tsaye.

'TikTok ya zama wajen ta’addanci,' Bukarti

A cewar Bukarti, ya zama wajibi a hada kai da kamfanin TikTok domin toshe asusun da 'yan ta'addan ke amfani da su.

Ya ce:

“Ko da ba za a iya bin sawun kowanne dan ta’adda ba, ya kamata hukumomin leken asiri da tsaro su hada kai da TikTok domin rufe akawun din 'yan ta'addan.”

Ya jaddada cewa shiru ko jinkiri daga bangaren hukumomi kan lamarin barazana ce ga zaman lafiya.

Ya kara da cewa gazawar da ake samu daga shugabanni ce ta bai wa ‘yan ta’adda damar bayyana kai a kafafen sada zumunta ba tare da tsoro ba.

Bukarti
Bukarti ya yyi martani wa dan Boko Haram da ya masa barazana. Hoto: Audu Bulama Bukarti
Asali: Twitter

Bukarti ya yi martani bayan masa barazana

Bayan wani dan Boko Haram ya aika da barazana gare shi a bidiyo, Bukarti ya mayar da martani da cewa:

“Karnukan Shekau sun fara biyo ni da haushi. Ina ganin akwai bukatar a tuna masa yadda muka yi da babansu... Shi ma haka ya bar mu da yardar Allah.”

Ya cigaba da caccakar shugabanni da cewa:

“Idan ma ban da lalacewar shugabanninmu, ta yaya ‘yan ta’adda za su fito kafafen sada zumunta..., har bidiyo kai tsaye suke yi kuma jami’an tsaro suna kallo?”

Sarakunan Arewa sun yi taro kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa sarakunan Arewa sun yi wani taro na musamman kan tsaro a Arewacin Najeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ne ya jagoranci zaman a dakin taron da ke fadar gwamnatin Borno.

Sarkin Musulmi ya bukaci shugabannin siyasa da na gargajiya su hada kai domin samar da mafita ga ta'addanci da ya addabi Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng