"Za a Kara Dagula Rashin Tsaro," Gwamnan Jigawa Ya Soki Shawarar Janar TY Danjuma
- Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa kiran da ake yi wa 'yan Najeriya da su dauki makamai su kare kansu zai haifar da matsala
- Tsohon Ministan tsaro, Theophilus Danjuma ya shawarci mazauna Filato da Binuwai su tashi haikan domin kare rayukansu daga harin 'yan ta'adda
- Mai girma Namadi ya kare gwamnatin tarayya, yana mai cewa ana ɗaukar matakai daban-daban don magance matsalolin tsaro a fadin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yi watsi da kiran da ake yi wa ‘yan Najeriya da su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai irin wannan matsayi da za a bukaci mutane su dauki doka a hannunsu da sunan kare rayukansu ba.

Asali: Facebook
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, Gwamna Namadi ya bayyana cewa kiran da ake yi na kare kai na iya haifar da rudani da tabarbarewar doka da bude kofar fitina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan martanin na Gwamna Namadi ya biyo bayan kalaman da tsohon Ministan tsaro, Theophilus Danjuma na cewa jama’a a Binuwai da Filato da su kare kansu daga 'yan ta'adda.
Martanin gwamnan Jigawa ga TY Danjuma
Vanguard News ta ruwaito gwamnan Jigawa ya ce kiran zai kara dagula al’amura, inda ya ce akwai hanyoyi da dama da gwamnati ke amfani da su domin shawo kan matsalar tsaro.
Gwamnan ya ce:
“Shi (Danjuma) mutum ne mai fahimta sosai kan harkar tsaro, amma ni a ra’ayina, idan ka bar mutane su kare kansu, za a fada cikin rudani. Gwamnati tana iyakar kokarinta wajen samar da tsaro da tsarin tsare lafiyar al’umma.”
Gwamnan Jigawa ya ba shawara kan tsaro
Gwamna Umar Namadi ya ba da misali da yadda ya magance rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa, ya ce da ya amince mutane su kare kansu, da rikicin ya fi kamari.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Kamar yadda na fada, abin da muka yi a Jigawa, da mun bar mutane su kare kansu, hakan zai janyo babbar matsala tsakanin manoma da makiyaya.
Amma lokacin da muka hau mulki, mun aiwatar da hanyoyi da dama ciki har da tattaunawa, da kuma shiga tsakani tare da sarkin gargajiya da masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu.”
Gwamnan ya kara da cewa bayan shawarwari da bangarorin da abin ya shafa, an kafa kwamiti domin daidaita al’amura da warware matsalolin da ke haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
An ba 'yan Najeriya shawarar dakile rashin tsaro
A wani labarin, kun samu labarin cewa tsohon Ministan tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya), ya bayyana damuwarsa kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Ya ce lokaci ya yi da 'yan kasar nan za su tashi tsaye domin kare kansu, domin gwamnati ba za ta iya yin komai ita kaɗai ba wajen shawo kan matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa.
Janar Danjuma ya bukaci jama’a su rika zama cikin shiri da lura da abin da ke faruwa a kusa da su, tare da amfani da duk wata hanya ta kare kai da za ta hana hare-haren a yankunansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng