Ana Fama da Boko Haram, Sarkin Musulmi Ya Sanar da Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda

Ana Fama da Boko Haram, Sarkin Musulmi Ya Sanar da Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, uhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana kafafen sada zumunta matsayin ƙungiyoyin ƴan ta'adda
  • Sa'ad Abubakar III ya koka kan irin yadda ake ƙirƙirar labaran ƙarya waɗanda za su iya haifar da rikici daga kafafen sada zumuntar
  • Sultan ya yi kira ga hukumomin tsaro kan su yi gaggawar ɗaukar matakan da suka dace kan barazanar da kafafen ke haifarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya bayyana kafafen sada zumunta a matsayin ƙungiyar ƴan ta’adda.

Sarkin Musulmin ya buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa kan barazanar da suke kawowa.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya ce kafafen sada zumunta kungiyoyin 'yan ta'adda ne Hoto: Ningi Emirate
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na majalisar sarakunan gargajiya na Arewa da aka gudanar a Maiduguri a jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sarkin Musulmi ya ce kan kafafen sada zumunta?

Sarkin Musulmin ya buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki kafafen sada zumunta da muhimmanci kamar yadda suke daukar sauran barazanar da ke addabar tsaron ƙasar nan.

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya caccaki kafafen sada zumunta saboda yaɗa labaran karya da ka iya haddasa rikice-rikice a cikin al’umma, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

“Abin da ya faru ya faru. Ba za ka zo kana yin magana kan kafafen sada zumunta ba, domin wannan wata ƙungiyar ƴan ta’adda ce."
"Kafafen sada zumunta ƙungiyar ƴan ta’adda ce. Abin da suke yi, mutum zai zauna a gida yana kwance ya ƙirƙiri labarai, daga bisani kuma a gano cewa ba gaskiya ba ne."

- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Kiran da Sarkin Musulmin ya yi na ɗaukar mataki ya nuna muhimmancin hana yaɗa labaran ƙarya, waɗanda ya ce mutane ke ƙirƙirowa cikin sauki a yanar gizo.

“Saboda haka, kafafen sada zumunta ƙungiyoyin ta’adda ne da dole ne mu magance su."
"Dole ne hukumomin tsaro su magance wannan ƙungiyar ƴan ta’addan da ake kira kafafen sada zumunta."

Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi ya koka kan rashin tsaro

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya damu.kan rashin tsaro Hoto: Ningi Emirate
Asali: Facebook

Har ila yau, Sarkin Musulmin ya yi Allah-wadai da rikice-rikicen da ake ci gaba da yi a jihar Plateau da wasu sassan ƙasar nan.

Ya buƙaci shugabannin siyasa da hukumomin tsaro da su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalolin.

Sarkin Musulmin ya soki yadda ake ci gaba da fitar da sanarwar Allah-wadai ba tare da ɗaukar wani mataki ba, yana mai jaddada bukatar aiwatar da matakan da suka dace don kawo ƙarshen tashe-tashen hankula.

Sarkin Musulmi ya ba da lambar yabo

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ta ba da lambar yabo ga wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Fadar Sarkin Musulmin ta ba da kyauta mai tsoka ga matasan ƴan NYSC saboda sadaukarwar da suka yi lokacin hidimtawa ƙasa.

Shugaban NYSC na jihar Sokoto, ya ce an ba da kyaututtukan ne domin ƙarfafa gwiwar matasa su zauna su hidimtawa ƙasa a yankunan karkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng