Mahmuda: Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Fara Kashe Mutane a Arewa ta Tsakiya

Mahmuda: Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Fara Kashe Mutane a Arewa ta Tsakiya

  • Sabuwar kungiyar ta’adda mai suna Mahmuda ta fara addabar kauyuka a yankin da ke kusa da filin shakatawa na Kainji a Kaiama da Baruten a jihar Kwara
  • Rahotanni sun ce ‘yan kungiyar na tilastawa mazauna yankin su biya haraji domin su samu damar noma, farauta da kasuwanci, kuma sun fara kisan kai
  • Mutanen yankunan sun bayyana fargabarsu game da barazanar tsaro da kuma tasirin hakan ga amfanin gona, yayin da hukumomi suka yi shiru kan lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Al’ummar wasu sassan jihar Kwara da Jihar Neja sun fara shan wahala daga sabuwar kungiyar 'yan ta’adda da ake kira Mahmuda.

An ruwaito cewa kungiyar ta fara tayar da hankali a yankunan da ke makwabtaka da filin shakatawa na Kainji.

Yan ta'dda
Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bulla a Arewa. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa kungiyar ta addabi kauyukan yankin Yashikira a Baruten, da Kemaanji, Wajibe da Nuku a Kaiama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa kungiyar na barazanar hana manoma zuwa gonakinsu, inda suka ce hakan na kawo babbar illa ga amfanin gona da zaman lafiya.

Punch ta wallafa cewa ayyukansu sun kai har yankin Babana da Wawa na karamar hukumar Borgu da ke Jihar Neja.

Ta'addancin da sabuwar kungiyar ke yi

Wani tsohon dan majalisa daga daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa ya bayyana cewa kungiyar Mahmuda ta kwace iko da dukkan harkokin yau da kullum a yankin.

Ya ce lamuran da suka hada da noma, farauta, kamun kifi da kasuwanci duk suna hannun 'yan kungiyar.

A cewarsa:

“Sun amince da a ci gaba da aiki da sharadin a rika biyansu wani kudi. Suna amfani da kudin wajen sayen makamai.

"Sun kai wa masu gadin gari da masu farauta hari, sun kashe sama da mutum 10.”

A cewarsa, cikin makon nan ne suka sake kai wani hari na karshe, lamarin da ya kara dagula lamarin tsaro a yankin.

Halin da ake ciki bayan bullar kungiyar Mahmuda

Wani mazaunin Kaima, Muhammad Ahmed, ya bayyana cewa sababbin hare-haren da suka faru na ramuwar gayya ne, sakamakon harin sama da sojoji suka kai wa mafakar kungiyar a daji.

Ya ce:

“Sun yi wa mafarauta da masu gadin gari dirar mikiya, sannan suka fitar da gargadi cewa kada a koma gona, saboda suna zargin mazauna yankin na ba da bayanai ga jami’an tsaro.”

Ko da aka yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara, ba a samu amsa daga kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ba.

Sai dai a baya-bayan nan, rundunar ta musanta labarin cewa wasu ‘yan bindiga daga Zamfara sun kafa sansani a garin Baruten.

Janar Musa
An bukaci magance sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ta bulla a Arewa. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

An kama mahaifin kan cin zarafin 'dan shi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani mahaifi kan cin zarafin dan shi mai shekaru 7.

Baya ga mahaifin, gwamnatin ta tabbatar da kama kishiyar mahaifiyar yaron domin cigaba da bincike.

Legit ta rahoto cewa an kama mutanen ne bisa zargin yi wa yaron horon da ya kai ga yanke masa kafafu a kan laifin daukar biskit.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng