Kazamin Fada Ya Barke Tsakanin Kwamandojin ISWAP, an Kashe 'Yan Ta'adda da Dama
- Rayukan mayaka da dama sun salwanta bayan an samu barkewar rikicin cikin a kungiyar 'yan ta'addan ISWAP
- Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya rikide zuwa musayar wuta bayan an samu sabani tsakanin wasu kwamandojin kungiyar
- Mummunan rikicin dai a fara ne bayan an samu takadda tsakanin kwamandojin kungiyar ta'addancin kan wani hari da aka tsara kaiwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Mummunan rikicin cikin gida ya barke a kungiyar 'yan ta'addan ISWAP don neman madafun iko a yankin da take da ƙarfi na Timbuktu Triangle.
An kashe mayaka da dama bayan da kwamandoji abokan gaba suka budewa juna wuta sakamakon saɓani a kan wani hari da aka tsara kaiwa.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Yadda aka gwabza fada tsakanin 'yan ISWAP
Majiyoyin sirri sun ce arangamar ta auku ne ranar Juma'a, 26 ga watan Yunin 2026, biyo bayan takaddama mai zafi da ta ɓarke tsakanin manyan kwamandojin a kan yadda za a gudanar da wani samame da aka tsara gudanarwa a daren da ya gabata.
Bisa ga majiyoyin, ɗaya daga cikin kwamandojin, wanda aka gano da sunan Abu Ali kawai, ya ƙi amincewa da barin mayakan da ke ƙarƙashin ikonsa su shiga cikin harin da aka tsara kaiwa.
An ce matakin nasa ya fusata wani babban kwamandan na daban, wanda ya zarge shi da kokarin gurgunta samamen tare da sanya ayar tambaya a kan amincinsa ga ƙungiyar.
An yi musayar wuta
Abin da ya fara a matsayin muhawara tsakanin ɓangarorin biyu ya rikide cikin sauri zuwa musayar harbin bindiga a cikin mazaunin ƙungiyar da ke Timbuktu Triangle, wanda shi ne ɗaya daga cikin mafi kariya a mafakar ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan
Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane
Majiyoyin sirri da dama da ke da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a yankin sun ce an kashe mayaka da dama lokacin fafatawar, yayin da ake amanna cewa ɗaya daga cikin kwamandojin ya mutu sakamakon raunin da ya samu a arangama.
Hukumomin tsaro har yanzu suna aiki domin gano fuskokin waɗanda ke da hannu a lamarin da kuma ƙayyade cikakken adadin mutanen da suka rasa rayukansu.
A kan yi fadan cikin gida tsakanin 'yan ISWAP
Lamarin ya nuna ɗaya daga cikin mafi munin lokuta na fadan cikin gida da aka yi a cikin ISWAP a cikin watannin nan na kwanan nan.
Majiyoyi sun ce saɓanin bai kasance kawai rashin jituwa ba, a'a, ya kasance ya ginu ne bayan haɓakar takaddama tsakanin kwamandoji a kan shawarwarin aiki, raguwar albarkatu, da kuma gudanar da harkoki cikin sansanin.

Source: Original
Majiyoyin sun amanna cewa ƙin amincewa da harin da aka tsara kaiwa ta fito da mafi zurfin koke-koke waɗanda suka daɗe suna taruwa a cikin ƙungiyar, inda kwamandoji ke ƙara yin gasa don neman tasiri, ƙarfin ma'aikata, da kuma ikon sarrafa kayayyaki.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yammasun kashe mutane biyu da ake zargi 'yan ta'addan Lakurawa ne a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta shigo Arewacin Najeriya? 'Yan sanda sun gano gaskiya
Hazikan dakarun sojojin sun kuma sun ƙwato makamai da harsashi yayin wani samame da suka kai a yankin Sabarumawa da ke jihar.
Hakazalika, dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, rumbun adana harsashi na AK-47 guda biyu, harsasai guda 143, da kuma babur guda ɗaya daga wurin da lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng
