Takarar Gwamna: Yadda Jam'iyyar ADC Ta Tsumbula cikin Rikicin Gida a Jihar Katsina
- Tsarin maslaha da jam’iyyar ADC ta runguma wajen tsaida ‘yan takara a jihar Katsina ya bar baya da kura
- Wasu masu neman takarar gwamna a ADC ba su gamsu da yadda aka ba Ahmad Babba Kaita tikiti a jam’iyyar ba
- Ba a gama shawo kan Mustapha Inuwa da Lawal Daura bai sai aka ji bullar takarar Salisu Lawal Uli a Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Tashen da jam’iyyar ADC ta fara ya gamu da babban kalubale a jihar Katsina sakamakon rikicin neman takarar gwamna a zaben 2027.
Manyan ‘yan siyasa da jagororin hamayya sun rungumi jam’iyyar, amma lissafi ya fara canzawa tun daga lokacin zaben tsaida ‘yan takara a Katsina.

Source: Facebook
Katsina: Rikici ya biyo bayan neman tikitin ADC
Wani dogon rahoto na jaridar Daily Trust ya yi bayanin yadda jam’iyyar ta samu kan ta a cikin wani yanayi na rigima da bangarewar shugabanci.
Barakar da aka samu ta jawo bangarorin Musa Wamba da Lawal Tukur Batagarawa suna ikirarin cewa su ne ainihin shugabannin ADC a Katsina.
A sakamakon haka aka samu Salisu Lawal Uli ya fito yana ikirarin shi ne ‘dan takarar gwamna yayin da a gefe guda ake da Ahmad Babba Kaita.
Wasu ‘yan taware ne suka shirya zabe kuma aka ba Salisu Lawal Uli tutar ADC a jihar ta Katsina.
Kan masu neman takarar gwamnan Katsina ya rabu
A gefe guda kuwa, jam’iyyar hamayyar ta yi yunkurin fitar da ‘yan takara a Katsina ta hanyar yin sulhu maimakon a shirya zaben tsaida gwani.
Wannan hanya da aka bi ya kara haifar da sabani musamma tsakanin irinsu 8 da Lawal Daura masu neman tikitin gwamna.
DCL Hausa ta rahoto Mustapha Muhammad Inuwa yana watsi da matsayar da aka cin ma bayan jin cewa Ahmad Babba Kaita ne zai yi takarar gwamna a badi.
Tsohon sakataren gwamnatin bai da matsala da Ahmad Babba Kaita, sai dai ya nemi ADC ta yi adalci. Tuni har an fara jin APC ta na zawarcin ‘dan siyasar.
Shi ma Lawal Daura wanda ya taba rike shugabancin DSS bai gamsu da takarar Sanatan Arewacin Katsina da ADC ta ba shi ba, har yana tunanin zuwa kotu.
Daura yana ganin ba a bi doka wajen ba tsohon ‘dan majalisar wakilan takarar gwamna ba.

Source: Facebook
Akwai aiki gaban jam'iyyar ADC a Katsina
Duk da farin jinin Babba Kaita, har yanzu bai iya shawo kan fusatattun masu neman takara ba, akasin abin da aka gani a APC a shekarun baya.
Idan aka tafi a haka, masu nazarin siyasa suna ganin ADC tana cikin babban hadari musamman ganin karfin mutane irinsu Mustapha Inuwa.
Sakamakon kakaba ‘yan takaran, wannan ya jawo wasu masu neman kujerun majalisar wakilan tarayya suka sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.
PDP ta hadiye wasu 'yan ADC a Katsina
A farkon watan Yunin 2026, labari ya zo cewa wasu mutane sama da 30 da suka nemi tikitin takara a ADC sun koma jam'iyyar PDP a jihar Katsina.
Legit Hausa ta lura da yadda kokarin gamsar da ‘yan takara ya jawo an rasa wasu mabiya sakamakon mika wa masu neman gwamna tikitin sanata.
ADC ta nemi wasu da ke neman zama sanata su yi takarar majalisar wakilan tarayya, su kuma masu neman zuwa majalisar sun tashi a tutar babu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

