Hankulan Mutane Sun Kwanta, Sojoji Sun Hallaka Rikakken Ɗan Bindiga a Zamfara

Hankulan Mutane Sun Kwanta, Sojoji Sun Hallaka Rikakken Ɗan Bindiga a Zamfara

  • Rundunar Sojoji sun yi kwanton bauna, suka hallaka Ibrahim Kaboni da wasu ‘yan bindiga a wajen garin Tsafe da ke jihar Zamfara
  • Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar 16 ga Afrilu yayin wani samame da dakarun Operation FANSAN YANMA ke yi
  • An yi kwanton baunar ne na hadin gwiwa da jami’an tsaro daban-daban wanda ya yi ajalinsa bayan sa ido na tsawon lokaci kan motsin ‘yan bindigar
  • Kaboni na cikin jerin masu laifi da ake nema ruwa a jallo kan kai hare-hare, satar shanu da garkuwa da mutane a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tsafe, Zamfara - Dakarun Sojojin Operation FANSAN YANMA sun kuma Murƙushe wani hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi al'umma.

Sojojin sun kashe shahararren dan bindiga, Ibrahim Kaboni, tare da mayakansa takwas a wajen garin Tsafe da ke Zamfara.

Sojoji sun ga bayan hatsabibin ɗan bindiga a Zamfara
An aika shahararren dan bindiga lahira a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa kwanton baunar ta faru ne da yammacin ranar 16 ga Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka aika dan bindiga lahira a Zamfara

Har ila yau, mun ruwaito muku cewa jami'an sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Kachalla Bello Kaura a kauyen Goburawar Dawan Jiya da ke karamar hukumar Anka a Zamfara.

Kaura da mayakansa sun mutu a wani samame da dakarun Fansan Yamma suka kai cikin mako guda a maboyarsu kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Kachalla Kaura ya yi kaurin suna da kai hare-hare a kauyukan da ke Zamfara, Kebbi da Sokoto, kuma yana da alaka da 'yan kungiyar Ansaruddin.

Bayan rasuwar Shadari, Kaura ya karbi jagoranci, yana kai farmaki a Anka, Bukkuyum, Gummi da kuma yankunan kan iyakar Kebbi da Sokoto.

Rikakken ɗan bindiga ya rasa ransa a Zamfara
Sojoji sun kawo karshen rikakken dan bindiga a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Yadda dan bindigar ya addabi al'ummar Zamfara

Wannan hari na musamman ya gudana ne bisa hadin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro bayan dogon sa ido kan 'yan bindigar.

Majiyar ta ce rikici ya barke yayin kwanton baunar, inda sojoji suka fatattaki 'yan bindigar, suka kashe Kaboni da mukarrabansa.

Ibrahim Kaboni yana cikin jerin sunayen da hukumomin tsaro ke nema kan hare-hare, satar shanu da garkuwa da mutane a Tsafe da kewaye.

Al'umma sun samu kwanciyar hankali a Zamfara

Kisan dan ta'addan ya kwantarwa al'ummar yankin hankali duba da barnar da yake ga mutane da kuma kitsa sace manyan mutane a yankin bayan hallaka da dama.

An tabbatar da cewa hakan zai sake kashewa sauran miyagu guiwa a yankunan da ke fama da hare-haren yan bindiga.

An kashe ɗan bindiga a Zamfara

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa faɗa kan mace ya jawo sanadiyyar hallaka wani rikakken ɗan bindiga, Kachalla Namadi wanda ya addabi mutane a jihar Zamfara.

Wasu ƴan bindiga da ke saɓani da Kachalla Namadi kan wata bazawara ne suka yi masa kwanton ɓauna sannan suka hallaka shi.

Saɓaninsu ne dai ya samu asali ne bayan Kachalla Namadi ya haƙiƙance cewa sai ya auri bazawarar wani ɗan bindiga da aka kashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.