'Yan Boko Haram Sun Kai Hare Hare a Adamawa, Sun Yi Barna Mai Yawa

'Yan Boko Haram Sun Kai Hare Hare a Adamawa, Sun Yi Barna Mai Yawa

  • Ƴan ta'addan Boko Haram masu tayar da ƙayar baya sun kai wasu sababbin hare-haren ta'addanci a jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Miyagun ƴan ta'addan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Hong inda suka hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
  • Ƴan ta'addan sun kuma ƙona gidaje da kadarori masu yawa a harin ta'addancin da suka kai a ƙauyukan masu makwabtaka da juna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Adamawa.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kashe mutane shida a harin da suka kai ƙauyukan Banga da Larh da ke cikin ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Adamawa
'Yan Boko Haram sun kashe mutum 6 a Adamawa Hoto: @OfficialAUF
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin wanda ya auku a ranar Talata ya shafi fararen hula da jami’an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Boko Haram sun yi ta'asa a Adamawa

A cewar majiyoyi daga yankin, an kashe maza biyu a Banga, sannan an hallaka wata mace guda ɗaya.

Majiyoyin sun ƙara da cewa a ƙauyen Larh da ke makwabtaka da Banga, an sake kashe wasu mutane biyu.

Wani ɗan sa-kai ya rasa ransa lokacin da wani bam ya fashe a yayin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin.

A wani lamari na daban, wata motar sintiri ta ƴan sanda daga Garaha da ke aiki a Banga ta tarwatse sakamakon fashewar wani bam.

Abin farin ciki, babu jami’in da ya ji rauni, domin sun bar motar ne kafin bam ɗin ya tashi.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Hong, Hon. Usman Wa’aganda, ya bayyana cewa har yanzu ana neman mutum ɗaya da ba a gani ba.

Ahmadu Umaru Fintiri
'Yan Boko Haram sun yi barna a Adamawa Hoto: @OfficialAUF
Asali: Facebook

Usman Wa'aganda ya ƙara da cewa ƴan ta’addan sun ƙona gidaje da kadarori masu yawa.

Harin ya ƙara tayar da hankula kan yunƙurin dawowar ayyukan Boko Haram a jihar Borno da ke makwabtaka da Adamawa.

A kwanakin baya ne gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana fargabar dawowar ayyukan Boko Haram, inda ya buƙaci ɗaukar ƙarin matakan tsaro domin daƙile barazanar.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojoji ta 23 Brigade, A. S. Adewunmu, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko dawo da amsar saƙonnin da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Sojoji sun gwaɓza da Boko Haram a Adamawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi ƙazamin artabu da ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Adamawa.

Fafatawar ta auku ne bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki kan sojoji yayin da suke aiki a wani shingen bincike da ke Garkida cikin ƙaramar hukumar Gombi.

Bayan an kwashi lokaci ana artabu, dakarun sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan ta'addan zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng