Abu Ya Girma: An Farmaki 'Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar AA a Wurin Jana'iza
- Jam'iyyar AA ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa ɗan takararta na shugaban kaa a zaben 2027, Aare Adekunle Rufai Omoaje
- Rahotanni sun nuna cewa an farmaki dan takarar AA ne yayin da rikici ya barke tsakanin magoya baya kungiyoyin siyasa a jihar Osun
- AA ta bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan lamarin, tare da gurfanr da duk wanda aka kama da hannu a harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Shugaban jam’iyyar AA na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Aliyu, ya yi Allah wadai da rahotannin harin da aka kai wa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Aare Adekunle Rufai Omoaje.
Alhaji Ibrahim ya bayyana farmakin a matsayin barazana ga ƙimar dimokuraɗiyya da siyasa cikin lumana a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Ledership ta ruwaito cewa rahotanni sun nuna cewa an kai wa Aare Adekunle Rufai Omoaje hari ne a ranar Asabar da ta gabata yayin da ya halarci wata jana’iza a jihar Osun.
An ce lamarin ya faru ne bayan rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan wasu ƙungiyoyin siyasa masu adawa, lamarin da ya tilasta wa ɗan takarar shugaban kasa na AA barin wurin domin tsira da lafiyarsa.
Jam'iyyar AA ta yi Allah wadai da lamarin
A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar a Zamfara ya fitar ranar Lahadi, AA ta ce bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya rikide zuwa tashin hankali ko tsoratarwa ba, ko da kuwa jam’iyyun da abin ya shafa sun bambanta.
Aliyu ya ce duk wani ɗan siyasa yana da damar ganawa da magoya bayansa da kuma neman cika burinsa na siyasa ba tare da fargabar rasa lafiyarsa ba.
Ya ƙara da cewa haƙuri da mutunta mabambantan ra’ayoyi na daga cikin ginshiƙan dimokuraɗiyya, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
AA ta bukaci bincike kan lamarin
Shugaban AA na Zamfara ya ce duk wani mataki da zai haifar da fargaba a fagen siyasa na iya raunana amincewar jama’a da tsarin zaɓe tare da rage sha’awar al’umma wajen shiga harkokin siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Source: Original
Jam’iyyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a ciki bisa tanadin doka.
A cewar sanarwar, kare ’yancin siyasa da kuma bai wa jam’iyyun adawa damar gudanar da ayyukansu cikin walwala na daga cikin muhimman nauyin da ke kan kowace al’umma mai bin tsarin dimokuraɗiyya.
An harbi ɗan APC a jihar Osun
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbi wani ’dan jam'iyyar APC, Taofeek Mustapha a jihar Osun.

Kara karanta wannan
'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'
Lamarin ya faru ne a yankin Oluode-Aranyin, inda wani mazaunin yankin, Sola Hammed, ya ce maharan sun iso cikin wata mota kirar Toyota Sienna mai ruwan kasa.
Jigon APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka farmake shi.
Asali: Legit.ng

