2027: An Miƙa Bukata ga Kwankwaso da Obi bayan An Fara Jita Jitar Za Su Fice daga NDC

2027: An Miƙa Bukata ga Kwankwaso da Obi bayan An Fara Jita Jitar Za Su Fice daga NDC

  • Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson ya fara roƙon yan takarar jam'iyyar kada su sauya sheka bayan hukuncin kotu
  • Hakan na zuwa ne bayan an fara rade-radin cewa 'yan takarar NDC na duba yiwuwar canza jam'iyya gabanin babban zaben 2027
  • Sanata Dickson ya tabbatar masu da cewa hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke ba zai hana su shiga zabe mai zuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya yi kira ga dukkan 'yan takara su yi hakuri su ci gaba da zama a cikin jam'iyyar bayan hukuncin babbar kotun tarayya.

Sanata Dickson ya bukaci ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, mataimakinsa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran yan takara kada su fice daga jam’iyyar a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan shari'ar NDC, ya aika sako ga magoya baya

Dickson.
Jagoran jam'iyyar NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson yana magana a taron NEC a Abuja Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Dickson ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Lahadi, yayin da yake martani kan rahotannin da ke cewa wasu 'yan takarar na tunanin ficewa daga NDC bayan hukuncin kotun.

Hukuncin kotu ya janyo rudani a NDC

Hakan na zuwa ne bayan Mai Shari’a Isah Dashen na Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ya soke hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, wanda ya umarci Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi wa NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kotun ta bayyana cewa hukuncin na farko ya shafi haƙƙin wata ƙungiya mai suna Peace Movement Party (PMP), wadda ta yi ikirarin mallakar tambarin da aka yi amfani da shi wajen neman rajistar NDC amma ba a haɗa ta cikin shari’ar ba.

Dickson ya roki 'yan takarar NDC

Sai dai Dickson ya yi watsi da rahotannin cewa 'yan takarar jam’iyyar sun shiga ruɗani bayan hukuncin, yana mai cewa har yanzu suna nan daram a cikin NDC.

Kara karanta wannan

'Za a kayar da Tinubu warwas a zaben 2027,' Sanata Dickson na NDC

A cewarsa:

"Abin da irin wannan hukunci yake son cimma shi ne ya haddasa ruɗani. Amma ina tabbatar wa dukkan mambobi cewa wannan ba shi ne halin da ake ciki ba.
"Yan takararmu za su shiga zaɓe, kuma sunayensu za su kasance a takardar zaɓe. Don haka babu abin da za a ji tsoro a kai."
Obi da Kwankwaso.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi tare da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Sanata Dickson ya zargi masu haddasa rikicin da ƙoƙarin karkatar da hankalin jam’iyyar NDC da kuma raunana ƙwarin gwiwar mambobinta, kamar yadda Punch ta kawo.

Ya ƙara da cewa:

"Ina tabbatar wa dukkan 'yan takararmu da mambobinmu cewa NDC tana cikin jam’iyyun da za su shiga zaɓe. Ba a soke rajistar jam’iyyar ba, kuma ba za a soke ta ba. Doka za ta yi aikinta, kuma adalci zai tabbata."

Kara karanta wannan

Dan takarar majalisa da jiga jigan NDC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

NDC ta bude kofar kulla ƙawance

A wani rahoton, kun ji cewa babban jagoran NDC a Najeriya, Sanata Seriake Dickson, ya ce jam'iyyar a shirye take ta tattauna da sauran jam'iyyun adawa game da hadaka.

Dickson yq ƙara da cewa NDC ba ta ɗauki kanta a matsayin wadda ta fi sauran ba, yana mai cewa ana sa ran za a fara tattaunawa mai zurfi bayan dukkan jam'iyyu adwa sun kammala zaɓen 'yan takararsu.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da jam'iyyun adawa ke ci gaba da ƙoƙarin ƙulla ƙawance mai ƙarfi kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262