'Yan Bindiga Sun Fusata da Ba Sojoji Bayanai, Sun Ƙaƙaba Harajin N60m ga Ƙauyuka
- Wasu 'yan bindiga sun tilasta wa ƙauyuka 12 a Maru da ke jihar Zamfara biyan harajin N60m bisa zargin ba sojoji bayani
- Sojoji sun kai farmaki maboyar 'yan ta’adda a dajin Dan Kurmi, inda suka kashe da dama daga cikinsu makon da ya gabata
- An ce 'yan ta’addan sun kira shugabannin ƙauyuka don tattaunawa, amma daga ƙarshe suka tilasta musu haraji don guje wa hari
- Hakan ya zama ruwan dare a Zamfara da jihohin makwabta inda 'yan ta'adda ke karɓar haraji don ci gaba da ta’addanci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun sanya wa ƙauyuka 12 a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara harajin N60m.
Mazauna yankin sun ce an kakaba harajin ne domin ladabtar da su bisa zargin su na bai wa sojoji bayanai.

Asali: Original
Kauyukan da yan bindiga suka sanya haraji
Premium Times ta ce sojoji sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’addan a dajin Dan Kurmi makon da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin ya tabbatar cewa an umarci mazauna Koloma, Dan Hayin Zargado da sauransu su biya kudin.
Sauran sun hada da ƙauyukan Zargado, Dan Godabe, Sabuwar Tunga, Makini, Bubaka, Yelwa, Bahwada, Koda, Manya da Kabusu.
Rahotanni sun ce 'yan ta’addan sun gayyaci shugabannin ƙauyuka don tattaunawa amma su ka ƙare da haraji.
Sarkin Dan Kurmi, Sani Usman, ya shaida wa yan jaridu cewa ‘yan ta’addan sun ce sun ƙona daji ne.

Asali: Facebook
Musabbabin sanya haraji da yan bindiga suka yi
An ce miyagun sun ɗauki matakin ne don hukunta mazauna ƙauyukan bisa kona dajin da ke kusa da maboyarsu a lokacin harin sojoji.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Zamfara, Abubakar Sadiq, bai amsa kiran wayarsa ba ranar Litinin da aka yi masa ba.
A jihar Zamfara da makwabtan jihohi, haraji daga ‘yan ta’adda ya zama ruwan dare don tallafa musu da ayyukan ta’addanci.
An ruwaito cewa ƙauyuka da dama a Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Neja da Kebbi sun fuskanci hare-hare saboda kin biyan haraji.
Har yanzu miyagu na ci gaba da cin karensu babu babbaka musamman kan ƙauyukan jihohin Arewa maso Yamma har ma da wasu a Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
A Arewa ta Tsakiyar Najeriya, yan bindiga sun addabi jihohin Kwara, Niger, Kogi, Benue, Plateau da sauransu wanda ya yi ajalin al'umma da asarar dukiya mai tarin yawa.
Zamfara: Sojoji sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga
A wani labarin, rundunar sojoji sun yi kwanton bauna inda suka yi nasarar hallaka Ibrahim Kaboni da wasu ‘yan bindiga a garin Tsafe da ke jihar Zamfara.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar 16 ga Afrilu yayin wani samame da dakarun Operation FANSAN YANMA ke yi domin kakkaɓe ƴan bindiga a yankunan.
Rahotanni sun ce Kaboni na cikin jerin masu laifi da aka jima ana nema ruwa a jallo kan kai hare-hare, satar shanu da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng