'Yan Ta'adda Sun Kutsa Makaranta a Borno, an Sace Daliban da ke Jarabawa
- 'Yan ta'adda da ake zargin mambobin kungiyar ISWAP/Boko Haram ne sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwamnati da ke Borno
- Miyagun sun tattara daliban da ke zana jarabawar NECO zuwa cikin daji tare da kashe wani malami guda daya a makarantar
- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa an tura jami'an tsaro domin ceto mutanen da aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - 'Yan ta'adda da ke ɗauke da makamai sun yi garkuwa da adadin ɗaliban da ba a kayyade ba a wata makarantar sakandare a jihar Borno.
'Yan ta'addan sun sace daliban ne a makarantar sakandaren gwamnati ta jeka ka dawo da ke garin Lassa, a yankin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Source: Original
Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa maharan sun afkawa makarantar ne a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Yunin 2026.
Maharan sun kai harin ne yayin da ɗalibai ke tsaka da zama domin rubuta jarabawar kammala sakandare ta Senior School Certificate Examination (SSCE) wadda hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ke shiryawa.
An ruwaito cewa an kashe ɗaya daga cikin malamai lokacin da lamarin ya auku, yayin da wani na daban ya samu raunuka.
'Yan sanda sun tabbatar da lamarin
A cewar rahoton jaridar The Punch, Nahum Daso, jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sandan jihar Borno, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa wasu ɗalibai har yanzu ba a gano inda suke ba.
“A yau da misalin ƙarfe 9:00 na safe, mambobin da ake zargi na 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun afkawa garin Lassa a kan babura."
“Adadin ɗaliban da ba a ƙayyade adadinsu ba har yanzu ba a gano inda suke ba a halin da ake ciki, amma 'yan sanda, sojoji, mafarauta da 'yan banga sun zagaye yankin."
- Nahum Daso
Ana sace dalibai a Najeriya
Wannan lamari ya ƙara yawan lokutan da aka sace yara 'yan makaranta a harabar makarantu ta hannun 'yan ta'adda.
Tsakanin ranakun 13 da 14 ga watan Mayun 2026, 'yan ta'adda sun afkawa wata makarantar firamare a Chibok, Borno, inda suka yi garkuwa da yara 42.

Source: Facebook
A ranar 15 ga watan Mayun 2026, kusan ɗalibai 39 da malamai bakwai aka yi garkuwa da su lokacin da 'yan bindiga suka afkawa makarantu guda uku a yankin Ahoro-Esiele/Yawota na Oriire a Ogbomoso, jihar Oyo.
Lamarin ya jawo fushi a wajen al'umma, wanda ya kai ga gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya na tsawon kwanaki biyu ta hannun mambobin kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) da sauran masu ruwa da tsaki.
An cafke shugabannin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomin tsaro sun kama mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne.
A cewar Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, an cafke kwamandojin ne bayan dawowarsu daga aikin Hajji na shekarar 2026.
Ministan ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan sun dawo daga Makka.
Asali: Legit.ng

