Gwamnan Filato Ya Fadi Wuraren da 'Yan Bindiga Suka Mamaye a Jiharsa
- Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya ce tun bayan komawar Najeriya zuwa mulkin dimokuraɗiyya jiharsa ke fama da rikici
- Ya ce hare-hare da tashe-tashen hankula sun zama ruwan dare a jihar, inda kowane yanki ke fama da irin nasa rikicin
- Mutfwang ya ce muhimman wurare da aka tanada domin ci gaban noma da kiwo da kuma kare muhalli sun koma maboyar miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa jihar ba ta taɓa samun cikakken tsaro ba tun lokacin da aka fara mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da manyan ‘yan jihar, ya ce ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun mamaye dazuka, filayen kiwo da wuraren ajiyar namun daji a fadin jihar.

Asali: Twitter
The Nation ta wallafa cewa Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki tare da fitattun ‘yan jihar dangane da jerin kisan gillar da aka yi a baya-bayan nan a jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Filato ya koka kan rashin tsaro
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa rahotannin sirri da suka samu sun tabbatar da cewa filin kiwo na Wase a karamar hukumar Wase na karkashin yan ta'adda.
Haka kuma wurin ajiyar namun daji na Pandam a karamar hukumar Qua’Pan, da wasu wurare, sun koma maboyar ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu miyagun laifuka.
Ya ce:
“Yau babu wani yanki a shiyyoyin Filato guda uku da jihar ke da su da bai fuskanci rikici ba. A Wase, alal misali, an kera filin kiwo tun zamanin Arewacin Najeriya, amma na tabbata, sama da shekaru 10 yanzu ba a iya shiga wannan yanki.”
'‘Yan ta’adda sun mamaye Kanam,' Gwamna
Gwamna Caleb Mutfwang ya ci gaba da bayyana cewa rahotannin da suka samu sun tabbatar da cewa har yankin Kanam ya shiga cikin matsanancin hali.

Asali: Twitter
Gwamnan ya ce:
“Rahotannin da muke samu daga wurin ajiyar namun daji na Pandam na da matuƙar tayar da hankali. Ya koma maboyar masu garkuwa da mutane da kuma wurin hada-hadar kudaden fansa. Yawancin garkuwa da mutane da aka yi a Shendam na da alaka da wannan wuri.”
Gwamna ya fadi maganin rashin tsaron Filato
Gwamna Mutfwang ya ce watakila daya daga cikin dalilan da yasa rashin tsaro ya yi kamari shi ne rashin haɗin kai da kuma rashin yin magana da murya ɗaya a matsayin ‘yan Filato.
Ya ce:
“Lokacin da rikicin ya fara, an ɗauke shi a matsayin matsalar Tarok. Daga bisani ya koma matsalar Berom. Yanzu, babu wanda ya tsira, amma har yanzu muna nuna kamar kowa ya yi ta kansa.”
Ya kara da cewa jihar ba za ta iya ci gaba ba sai an fuskanci babban matsalar da ke addabar ta tsawon shekaru fiye da ashirin da murya daya.
An yi zanga-zanga kan kashe-kashen Filato
A baya, mun wallafa cewa mutane da galibinsu Kiristoci ne sun ɓarke da zanga-zanga a Jos, babban birnin Jihar Filato domin nuna ɓacin rai da damuwa kan hare-haren 'yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren da ake kai wa musamman a ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 100 a cikin makonni biyu kawai.
Zanga-zangar ta fara ne a titin Fwavwei, inda daruruwan mutane suka taru tare da rufe hanyoyi, lamarin da ya haddasa cunkoso da tsaikon zirga-zirga a kokarinsu da mika kuka ga gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng