Gwamnatin Borno Ta Yi Martani kan Zargin Tura Tsofaffin 'Yan Boko Haram Aikin Soja

Gwamnatin Borno Ta Yi Martani kan Zargin Tura Tsofaffin 'Yan Boko Haram Aikin Soja

  • Gwamnatin jihar Borno ta yi raddi a kan rahoton da ke cewa ta dauki nauyin tura wasu tubabbun 'yan Boko Haram su shiga aikin soja a Najeriya
  • Ta bayyana cewa an dai yi aikin tantan cewa ne bayan rundunar sojin kasar nan ta fitar da sunayen wadanda zaba domin daukar su aiki
  • Hukumar jagoranci da bayar da shawarwari da ke aikin tantancewar ta bayyana cewa mutum 732 ne kacal suka tsallake siradin samun guraben aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Gwamnatin jihar Borno ta musanta rahoton da ke zargin cewa ta ɗauki nauyin wasu tsofaffin mayaƙan Boko Haram domin su shiga aikin rundunar Sojojin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto da ya yi ikirarin cewa tsofaffin mayaƙan Boko Haram 40 da aka zaɓa a cikin shirin ɗaukar sababbin sojoji na 91 (RRI) suna gudanar da gwajin lafiya a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Gwamnatin Zulum ta karyata daukan tubabbun yan Boko Haram su shiga aikin soja
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Source: Twitter

A hira da jaridar Premium Times, Babban Sakataren hukumar jagoranci da bayar da shawarwari, Mohammed Jimmeh, ya ce zargin ba shi da tushe.

Gwamnati ta karyata daukan tubabbun yan Boko Haram

A jawabinsa, Mohammed Jimmeh ya kara da cewa gwamnati ko hukumar ba su taɓa ɗaukar nauyi ko ba da shawarar a ɗauki wani tsohon ɗan ta'adda aikin soja ba.

A kalamansa:

"A'a, ba gaskiya ba ne. Ni ma abin ya ba ni mamaki lokacin da na ga rahoton, domin na kasance a wurin tantancewar tun daga farko."

Mohammed Jimmeh ya bayyana cewa mutane 3,036 daga jihar Borno ne aka fara zaɓa ta shafin yanar gizon rundunar sojoji domin shiga matakin tantancewa.

Aikin soja: An tantance yan Borno

Daga cikin mutanen da suka nemi aikin, mutum 2,100 ne suka halarci wurin tantancewar, amma mutum 732 ne kawai suka cika dukkannin sharuɗɗan bayan an binciki asalinsu, an yi masu gwajin lafiya da na ƙarfin jiki tare da sauran matakan tantancewa.

Kara karanta wannan

Hankulan mutane sun tashi kan yadda aka tsinci gawar budurwa a ɗakin saurayinta

Gwamnatin Borni ta ce ba ta da hurumin daukan jami'an soja
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalar 'yan Boko Haram Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

"A yanzu muna da mutum 732 da suka yi nasarar tsallake tantancewar, kuma za mu iya tabbatar da su da fuska da suna."

A cewarsa, masu neman aikin ne ke yin rajista da kansu ta shafin rundunar soji, yayin da aikin hukumar ya fara ne bayan an fitar da sunayen waɗanda aka zaɓa.

Ya ce jami'ai biyu daga kowace ƙaramar hukuma 27 ta jihar ne ke tabbatar da cewa masu neman aikin 'yan asalin yankunansu ne kafin su ci gaba da sauran matakan tantancewa.

Mohammed Jimmeh ya ƙara da cewa hukumar ba ta da bayanan tsofaffin mayaƙan Boko Haram da aka gyara tunaninsu, kuma ba ta da alhakin shirye-shiryen farfaɗo da su ko mayar da su cikin al'umma.

Sojoji sun jefa wa 'yan Boko Haram bama-bamai

A baya, kun samu labarin cewa Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun ci gaba da kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas domin dakile kaifin aikin ayyukan yan ta'adda.

Kara karanta wannan

An sauke wasu manyan sojojin Najeriya, an nada sababbin kwamandoji

Sojojin saman sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren da 'yan ta'adda suke samun mafaka yankin Metele na jihar Borno, inda suka yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da wasu manyan kwamandojinsu.

'Yan ta'adda sun sha kai wa dakarun Operation Hadin Kai da ke aiki a yankin kwantan ɓauna akai-akai kafin wannan samamen na baya-bayan nan na sojojin sama da ya ragargaza manyan cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng