'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kano, An Kashe Wasu bayan Garkuwa da Yaron Ɗan Kasuwa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kano, An Kashe Wasu bayan Garkuwa da Yaron Ɗan Kasuwa

  • Yan bindiga sun hallaka mutane biyu, sun sace wasu biyu a harin da suka kai Faruruwa a Kano da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Alhamis
  • Mazauna garin sun fada a cikin tashin hankali bayan da mutane, dauke da mugayen makamai suka shigar masu kasuwa, tare da harbin jama'a
  • Shugaban karamar hukumar Shanono, Abubakar Barau, ya tabbatar da an fara bincike tare da alkawarin ba da cikakken hadin kai ga jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban karamar hukumar Shanono da ke jihar Kano, Abubakar Barau, ya tabbatar da harin da wasu 'yan bindiga suka kai wa al’ummar Faruruwa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban karamar hukumar, Kwamred Ammar Wakili Shanono, ya fitar wa manema labarai da safiyar Juma'a.

Shanono
Yan bindiga sun kai hari Kano Hoto: Ammar Wakili Shanono
Asali: UGC

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook tun da farko, Ammar Wakili Shanono ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar ya yi tir da wannan hari matuka..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mummunan al'amarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da sace wasu biyu, yayin da ya jefa jama'a a cikin firgici.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano

Ammar Wakili Shanono ya tabbatar wa Legit cewa harin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Alhamis.

Ya ce wadanda ake zargi da satar mutane sun kutsa kasuwar unguwar Faruruwa dauke da makamai, inda suka harbe mutane biyu har lahira,.

Shanono ya kara da cewa haka kuma miyagu mutanen sun yi garkuwa da wasu mutum biyu, sannan suka raunata wasu guda biyu da yanzu haka ake kula da su a asibiti.

A cewarsa:

“Daya daga cikin gawarwakin ma ba a ganta ba a lokacin, sai daga baya aka gano gawar bawan Allah kwance a cikin daji, sun kashe shi.”

Za a yi binciken harin da aka kai a Kano

Shugaban karamar hukumar Shanono, Abubakar Barau, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda matsalar rashin tsaro ke karuwa a wasu sassan yankin, musamman a unguwannin da ke iyaka da Katsina.

Bindiga
Jama'ar Shanono jim kaɗan bayan jana'izar waɗanda yan ta'adda suka kashe Hoto: Ammar Wakili Shanono
Asali: UGC

Ya ce:

“Gwamnatinmu na kokarin tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Jami’an tsaro na gudanar da bincike a halin yanzu, kuma muna shirye tsaf don bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata a yayin binciken.”

Shugaban ya kuma bukaci al’ummar Faruruwa da su hada kai da jami’an tsaro domin a gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki, tare da hukunta su.

Hon. Abubakar Barau ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, yana addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ba su juriyar rashin da suka yi.

Hadimin gwamnan Kano ya rasu

A baya, mun wallafa cewa ana ci gaba da jimami a jihar Kano bayan rasuwar Abdullahi Salisu Furfura, wanda ya kasance mashawarcin Gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren harkokin matasa.

An bayyana Abdullahi Salisu Furfura a matsayin daya daga cikin matasan da suka tsaya tsayin daka wajen goyon bayan gwamnatocin Kwankwasiyya a lokuta daban daban a Kano.

A cikin sanarwar da aka fitar game da rasuwar Furfura, an bayyana cewa marigayin ya kasance jajirtacce mai kishin al’umma da matasa da neman ci gabansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.