Bayan Kai Hare Hare, Amurka da Iran Sun Dauki Sabuwar Matsaya kan Mashigar Hormuz

Bayan Kai Hare Hare, Amurka da Iran Sun Dauki Sabuwar Matsaya kan Mashigar Hormuz

  • Amurka da Iran sun amince da dakatar da hare-hare bayan musayar farmaki da ya kusa kawo tangarda ga yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Wani jami’in Amurka ya ce jiragen ruwa za su ci gaba da wucewa cikin Mashigar Hormuz cikin ‘yanci yayin da za a ci gaba da tattaunawa
  • Rahoton ya nuna cewa rikicin ya shafi muhimmiyar hanyar jigilar man fetur ta duniya bayan hare-haren da suka faru tsakanin bangarorin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Iran da Amurka sun amince da “dakatar da fada” bayan musayar hare-hare da aka yi tsakanin bangarorin biyu a cikin ‘yan kwanakin nan.

Wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa yanzu jiragen ruwa za su iya ci gaba da zirga-zirga cikin Mashigar Hormuz ba tare da takura ba.

Iran da Amurka sun tsagaita wuta bayan kai hare hare
Shugaban Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi (dama) Hoto: Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

A zantawarsa da kafofin yada labarai, jami'in ya ce za a ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran don kawo karshen yakin, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fada zai dawo: Trump ya yi gargadi mai tsauri kan Iran duk da maganar sulhu

Barazana ga yarjejeniyar tsagaita wuta

Sai dai har zuwa yanzu gwamnatin Iran ba ta fitar da sanarwa kan rahoton cewa ta amince da dakatar da hare-haren a mashigar ba.

A ranar 17 ga Yuni, Amurka da Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna mai matakai 14 (MoU), wadda ta kunshi dakatar da ayyukan soji a dukkan bangarori.

A cikin yarjejeniyar, Iran ta amince za ta yi amfani da dukkan kokarinta domin tabbatar da tsaron wucewar jiragen kasuwanci na tsawon kwanaki 60, a cewar rahoton Legit Hausa.

Sai dai yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma kasa da makonni biyu da suka gabata ta fuskanci barazana bayan bangarorin biyu sun sake zargin juna da kai hare-hare.

Rikicin Mashigar Hormuz ya tsananta

An sake fara kai hare-hare ranar Alhamis bayan wani makami da Iran ta harba ya kai hari kan wani jirgin dakon kaya a Mashigar Hormuz.

A karshen mako, Amurka ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wasu wurare a Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya jawo sabon fada da Iran ta kai hare haren kan Amurka

Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta ce farmakin martani ne ga abin da ta kira ci gaba da barazana ga jiragen kasuwanci.

Daga baya Iran ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait da Bahrain. Sai dai Amurka ta ce hare-haren ba su isa inda aka nufa ba, kuma babu rahoton asarar rayuka ko barna.

A baya bayan nan Iran da Amurka suka kaddamar da hare-hare kan juna game da mashigar Hormuz
Wani na nuna mashigar Hormuz da ke kusa da gabar tekun Iran a jikin taswira. Hoto: JULIEN DE ROSA / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Muhimmancin Mashigar Hormuz

Rahoton kafar watsa labarai ta Reuters ya nuna cewa Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur da iskar gas a duniya.

Tehran ta rufe hanyar ne bayan Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hare-hare kan Iran a karshen watan Fabrairu.

Saboda muhimmancin hanyar wajen samar da makamashi a duniya, duk wani rikici a yankin na iya shafar kasuwannin mai na duniya.

Trump ya yi sabon gargadi ga Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da ake maganar sulhu tsakanin Amurka da Iran, Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa kasar za ta iya sake ɗaukar matakin soja.

Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hare-hare kan wuraren ajiyar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, tare da cibiyoyin radar da ke bakin teku.

Ya yi barazanar cewa idan Iran ta ci gaba da hare-harenta, Amurka za ta dauki mataki, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta ci gaba da wanzuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com