Shugaban Matasa Ya Yi Barazanar Hallaka Waɗanda ba Su Son Jam'iyyar APC

Shugaban Matasa Ya Yi Barazanar Hallaka Waɗanda ba Su Son Jam'iyyar APC

  • Wani jagoran matasa a Delta, Henry Ufuoma Franklin, ya yi barazanar kashe duk wanda ya ƙi zaɓen APC a zaɓen 2027
  • Franklin ya gargaɗi masu goyon bayan jam'iyyun adawa da su guji rumfunan zaɓe a yankin Ndokwa, tare da barazanar haddasa tashin hankali
  • Bayan fuskantar suka, Franklin ya yi ikirarin cewa an ƙirƙiri bidiyon ta hanyar fasahar AI, amma binciken TheCable ya nuna akasin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Wani jagoran matasa a Delta, Henry Ufuoma Franklin, ya yi barazanar kashe mutanen da ba za su zaɓi jam'iyyar APC ba a zaɓen 2027 mai zuwa.

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Franklin ya gargaɗi masu adawa da APC a yankin Ndokwa da su guji zuwa rumfunan zaɓe a ranar zaɓe.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Gwamna ya yi wa al'ummarsa barazana game da zaben APC a 2027

Matashi ya yi barazana ga yan adawar APC
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta. Hoto: Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

Matashi ya yi barazana kan zaben APC

A cikin bidiyon, Franklin ya ce ya daɗe yana shiru duk da cin mutuncin da wasu ke yi wa shugabanninsa, amma yanzu ya yanke shawarar yin magana, cewar TheCable.

Ya ce:

“Ba na jin daɗin yadda lamarin yake faruwa. Wannan gargaɗi ne kai tsaye: idan ka san ba za ka zaɓi shugabannina daga sama har ƙasa ba, wato Tinubu, Sanata Okowa da Gwamna Sheriff, to ka nisanci zaɓen.
“Idan kana son zama gwauruwa, maraya ko rasa iyayenka, to ka guji wurin idan ba ka shirya zaɓen jam'iyyata ba, babbar APC, wadda ke son sauya Najeriya zuwa ƙasa mafi kyau.”

Haka kuma, jagoran matasan ya yi barazanar tayar da hankali idan wata jam'iyyar adawa ta gudanar da gangamin siyasa a yankin Ndokwa.

Franklin ya bayyana cewa shi cikakken ɗan jam'iyyar APC ne kuma zai ci gaba da kasancewa cikin jam'iyyar ko da kuwa ta sauya suna.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan APC suka ci dalolin Atiku amma suka zaɓi Buhari a 2015

Bidiyon ya bayyana ne kwanaki kaɗan bayan wasu 'yan bindiga sun kashe mutane shida a wani hari da aka kai wa tawagar kamfen ɗin Ovie Omo-Agege, ɗan takarar jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na kujerar sanatan Delta ta Tsakiya.

Dan APC ya yi al'umma barazana kan zabe
Taswirar jihar Delta da ke karkashin mulkin APC. Hoto: Legit.
Source: Original

An fara Allah-wadai da barazanar

Barazanar da Franklin ya yi ta janyo ce-ce-ku-ce da Allah-wadai a kafafen sada zumunta, musamman Facebook.

Yayin da ake ci gaba da sukar sa, Franklin ya fitar da wani bidiyo na daban inda ya yi ikirarin cewa fasahar AI ce ta ƙirƙiri bidiyon farko.

Jagoran matasan ya kuma zargi wasu mutane da kutse a shafukansa na sada zumunta, inda suka yi amfani da su wajen aikata damfara.

Sai dai binciken jaridar TheCable ya nuna cewa babu alamun amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar bidiyon da Franklin ya yi barazanar, sabanin ikirarin da ya yi.

Jaridar ta ce a bidiyon, Franklin ya yi magana da harshen Ukwuani cikin ƙwarewa, yayin da cikin motar da ya zauna a lokacin yin barazanar ya yi daidai da motar da ya yi amfani da ita wajen yin bidiyon musanta ikirarin.

Haka kuma, TheCable ta ce ta tantance bidiyon ta amfani da shafin Deploy Detect, wanda ke binciken abubuwan da aka ƙirƙira da fasahar AI.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan adawa, ya nuna ƙarfin da yake da shi a Arewacin Najeriya"

Sakamakon binciken ya nuna cewa bidiyon ba shi da alamun cewa an ƙirƙire shi da fasahar AI ko kuma aka yi amfani da fasahar wajen sauya hoton mutum.

Gwamna ya yi wa al'umma barazana kan zabe

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar hukunta al’ummar Amasiri idan suka ƙi zaɓen APC a babban zaɓen 2027.

Nwifuru ya yi gargaɗin cewa zai ɗauki mataki mafi tsanani kan mutanen idan ya sake samun nasara a zaɓen mai zuwa.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da barazanar da Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru a al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.