Gwamnatin Abba Ta Fadi Babbar Illar da Ta Yi wa Kwankwaso yayin Shiga APC

Gwamnatin Abba Ta Fadi Babbar Illar da Ta Yi wa Kwankwaso yayin Shiga APC

  • Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta tsoron tafiyar Kwankwasiyya, tana mai ikirarin cewa sama da kashi 70 cikin 100 na mambobin tafiyar sun koma jam’iyyar APC
  • Kwamishinan yada labarai na jihar, Sanusi Bature, ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, da kokarin bata wa Gwamna Abba Kabir Yusuf suna kan binciken da EFCC
  • Bature ya ce matsalolin Kwankwaso da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun fara ne tun shekaru 11 da suka wuce, kafin Abba Yusuf ya zama gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta tsoron tafiyar Kwankwasiyya, tana mai cewa tsarin tafiyar ya riga ya samu tangarda bayan da yawancin mambobinta suka koma jam’iyyar APC.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Sanusi Bature, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ɗebo ruwan dafa kansa bayan zargin Abba da shuna shi ga EFCC

Sanusi Bature da Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da Sanusi Bature a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A tattaunawa da Channels TV, Sanusi Bature kuma zargi tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, da kokarin bata wa Gwamna Abba Kabir Yusuf suna.

Abba ba ya tsoron Kwankwasiyya

Sanusi Bature ya ce tafiyar Kwankwasiyya ta rasa karfinta a Kano, yana mai ikirarin cewa sama da kashi 70 cikin 100 na mambobinta sun koma APC kuma suna aiki tare da jam’iyyar.

Kwamishinan ya ce:

"Babu wanda ke tsoron tafiyar Kwankwasiyya saboda tsarinta ya tarwatse. Mun karbi sama da kashi 70 cikin 100 na mambobinta zuwa APC, kuma suna yi wa APC aiki."

A bayanin da ya yi, Sanusi Bature ya ce wannan ne ya sa gwamnatin jihar ba ta ganin tafiyar a matsayin wata barazana ga siyasar APC a Kano.

Matsalar Kwankwaso da EFCC ta dade

Kwamishinan ya bayyana cewa Kwankwaso ya dade yana fuskantar matsaloli da EFCC da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC), tun bayan barinsa gidan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya tsoma Ganduje da Abba ke 'karar' Kwankwaso ga EFCC

A cewarsa, lamarin ya fara ne kimanin shekaru 11 da suka wuce, lokacin da Abba Kabir Yusuf bai ma fara tunanin zama gwamnan Kano ba.

Bature ya ce:

"Sanata Kwankwaso ya dade yana da matsala da EFCC da ICPC tsawon shekaru 11, tun bayan barinsa gidan gwamnatin Kano. A lokacin, Gwamna Abba Kabir Yusuf bai ma taba tunanin zama gwamnan jihar Kano ba."

Ya kara da cewa Kwankwaso ya sha samun gayyatar EFCC kuma ya ziyarci ofishin hukumar sau da dama.

Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NDC, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Bature ya kuma yi ikirarin cewa a shekarar 2024, tsohon gwamnan ya garzaya kotu a Kano domin neman umarnin hana EFCC kama shi.

Ga bayanin da Sanusi Bature ya yi:

Ministan tsaro ya ce yana APC

A wani labarin, kun ji cewa Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kare halartar tarukan siyasar APC, yana mai cewa ya yi ritaya daga aikin soja.

Musa ya ce duk da kasancewarsa dan APC, aikinsa na tabbatar da tsaro ya shafi dukkan jam’iyyun siyasa, ba jam’iyyar da yake ciki kadai ba.

Ya kuma yi alkawarin cewa ma’aikatar tsaro za ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da zaben 2027 cikin gaskiya da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng