APC Ta Yi wa Gwamna Ƙarfa Ƙarfa, Ta Cire Shi a cikin Kwamitin Kamfen Tinubu

APC Ta Yi wa Gwamna Ƙarfa Ƙarfa, Ta Cire Shi a cikin Kwamitin Kamfen Tinubu

  • Jam’iyyar APC a Osun ta kafa kwamitin mutum 168 domin yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Matakin ya biyo bayan kafa kwamitin mutum 344 da Gwamna Ademola Adeleke ya yi ba tare da manyan shugabannin APC ba
  • APC ta ce ba za ta amince da goyon bayan Tinubu kaɗai ba, tana son Adeleke ya goyi bayan dukkan ’yan takararta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun – Jam’iyyar APC a jihar Osun ta kafa wani kwamiti na musamman mai mutum 168 domin gudanar da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Matakin na zuwa ne yayin da ake samun rashin jituwa tsakanin shugabannin APC da Gwamna Ademola Adeleke kan rawar da zai taka wajen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jibga mutane 3000 a kwamitin yakin zabe don nasarar Tinubu da APC

APC ta watsa wa gwamna kasa a ido
Shugaba Bola Tinubu da Ademola Adeleke da sauran gwamnoninn Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

A baya-bayan nan ne Adeleke, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Accord, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu mai mutum 344 a birnin Osogbo, inda ya naɗa kansa jagoran kwamitin a jihar, cewar Punch.

Sai dai ƙaddamar da kwamitin ya gudana ba tare da manyan jiga-jigan APC ba, ciki har da tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Bola Oyebamiji, da shugaban APC na jihar, Tajudeen Lawal.

APC ta kafa sabon kwamitin mutum 168

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Lawal ya bayyana cewa jam’iyyar ta kafa sabon kwamiti ne domin tattara goyon baya ga sake zaɓen Tinubu da kuma tabbatar da nasarar ’yan takararta a zaɓen Majalisar Tarayya da ta jiha.

Jam’iyyar ta naɗa Bola Oyebamiji a matsayin darakta-janar na kwamitin, yayin da Tajudeen Lawal zai kasance mataimakinsa.

Kwamitin ya ƙunshi ’yan takarar sanata uku na APC, ’yan takarar Majalisar Wakilai tara, tsofaffin mataimakan gwamnoni huɗu, Janar Alani Akinrinade, Femi Fani-Kayode da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku ya gano kuskuren Tinubu a mulki, ya ɗauki alƙawarin gyara bangaren

APC ta bayyana dalilin kafa nata kwamitin

Lawal ya ce sun yanke shawarar kafa nasu kwamitin ne saboda rahotanni sun nuna cewa Adeleke ya bayyana aniyarsa ta goyon bayan Tinubu, amma ba zai yi wa sauran ’yan takarar APC kamfen ba.

Ya ƙara da cewa shugabancin APC ba zai amince da wannan matsaya ba, domin yana buƙatar dukkan mambobinta su yi aiki domin ganin Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar sun yi nasara a zaɓen 2027.

Wannan mataki ya ƙara bayyana rashin jituwar da ke ƙaruwa tsakanin shugabannin APC a Osun kan rawar da Adeleke ke takawa wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu.

Adeleke ya musanta yarjejeniya da APC

Mun ba ku labarin cewa Ademola Adeleke ya musanta cewa ya yi yarjejeniya da APC kan rabon kujerun majalisa da shugabancin ƙananan hukumomi a Osun.

Gwamnan ya ce haɗin gwiwarsa da fadar shugaban ƙasa na da alaƙa ne kawai da sake zaɓen Bola Tinubu a 2027.

Ya tabbatar da cewa zai goyi bayan ’yan takarar jam’iyyar Accord a zaɓen majalisar dattawa, wakilai da majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.