An Samu Rudani a APC da Mutane 2 Suka ‘Lashe’ Zaben Zama 'Dan Takaran Sanata

An Samu Rudani a APC da Mutane 2 Suka ‘Lashe’ Zaben Zama 'Dan Takaran Sanata

  • An samu kwamacala a zaɓen fitar da gwanin jam’iyyar APC na Sanatan Zamfara ta Arewa bayan hukuncin kotu
  • Jami’an zaɓe mabambanta sun ayyana Sahabi Ya’u da Tijjani Kaura a matsayin waɗanda suka samu tutar APC
  • Rikicin ya biyo bayan soke zaɓen farko da aka yi, sabanin Bello Matawalle da Abdulaziz Yari ya fito fili a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Zamfara - An samu ruɗani sosai daga zaɓen fitar da gwanin jam’iyyar APC na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa.

Jami’an zaɓe biyu sun bayyana Sahabi Ya’u da Tijjani Kaura a matsayin waɗanda suka yi nasarar samun takara.

Zamfara
Tijjani Kaura da Sanata Sahabi Yau Hoto: Dogon Kada ce/Salisu Wakkala
Source: Facebook

Fada a APC saboda takarar sanatan Zamfara

Daily Trust ta ce dama an samu rikici da hare-hare a wasu rumfunan zaɓe, lamarin da ya jikkata mutum da lalata dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Sanata mai ci ya sha kaye a sabon zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC ta gudanar

Rikicin nan ya biyo bayan soke zaɓen farko da kotu ta yi, yayin da bangarorin Bello Matawalle da Abdulaziz Yari su ke rigima.

A halin yanzu dai shugabannin jam’iyyar APC sun bayyana ’yan takara daban-daban a matsayin waɗanda suka yi nasara.

Zaɓen da aka gudanar ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, ya biyo bayan hukuncin kotu da ta soke zaɓen farko da aka yi.

Sakamakon zaɓen APC 2 masu karo da juna

Yanzu Sanata Sahabi Ya’u da tsohon Sanata Tijjani Yahaya Kaura ne suka fito a matsayin waɗanda suka samu tikitin APC.

A sakamakon farko da shugaban kwamitin zaɓen tsaida gwani na APC a yankin ya sanar, Sanata Sahabi Ya’u ya yi nasara.

Dr Auwal Abdullahi Aliyu, ya sanar da cewa Sahabi Ya’u ya samu ƙuri’u 49,176 a takarar tsaida gwanin.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Ya ce Tijjani Yahaya Kaura ya samu ƙuri’u 9,628, yayin da Sani Abdullahi Shinkafi ya samu 2,602 daga ‘ya ‘yan jam’iyya.

An samu wani 'dan takaran sanata dabam a APC

Sai dai wani jami’in zaɓe mai suna Sani Abdullahi shi ma ya sanar da wani sakamako daban, ya ba Tijjani Yahaya Kaura tuta.

A sakamakon na Sani Abdullahi, Kaura ya samu ƙuri’u 16,758, Sahabi Ya’u ya samu 1,465, yayin da Shinkafi ya samu 1,447.

Jaridar The Guardian tana cikin wadanda suka kawo labarin nasara Sanata Tijjani Kaura.

Wannan ya haifar da rashin tabbas kan wanda APC za ta amince da shi a matsayin ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Arewa.

Rigimar APC tsakanin Abdulaziz Yari da Bello Matawalle

Rahotanni sun ce ’yan takarar biyu da suka fito a sakamakon zaɓen suna da alaƙa da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC a Zamfara.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Barau Jibrin ya ce duk alamu na nuna Tinubu zai yi nasara a zaɓe

Sanata Sahabi Ya’u, wanda ke wakiltar Zamfara ta Arewa a Majalisar Dattawa, yana cikin ɓangaren Bello Matawalle da yake ministan tsaro.

Shi kuwa Tijjani Yahaya Kaura yana tare da tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari, wanda a yanzu shi ne Darakta Janar na kamfen APC.

Duka ’yan takarar biyu sun fito ne daga unguwar Galadima Dangaladima da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar ta Zamfara.

Majalisar Tarayya
Ginin Majalisar Tarayya a birnin Abuja Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Kotu ta maido wa APC aiki baya a Zamfara

An ji labari Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Sanata Sahabi Ya’u Kaura kan soke zaɓen fidda gwani na APC a Zamfara ta Arewa.

Alƙali ya tabbatar da hukuncin kotun tarayya da ya umarci APC ta sake gudanar da zaɓen tsaida gwani cikin kwanaki 14 a jihar Zamfara.

Kotun ta ce zaɓen farko bai bi ƙa’idoji da dokokin jam’iyyar APC ba don haka sai an yi wani sabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng