Sama da Kasa ba Za Su Hade ba idan Aka Hana Atiku Takara In ji Ministan Tinubu

Sama da Kasa ba Za Su Hade ba idan Aka Hana Atiku Takara In ji Ministan Tinubu

  • Festus Keyamo ya yi imanin cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa lafiya ko da Atiku Abubakar bai shiga takara ba
  • Kotun tarayya ta soke matakan da shugabannin ADC suka dauka. Ciki har da tsayar da Atiku a matsayin ɗan takara a 2027
  • Keyamo wanda lauya ne, ya ce ya kamata jam'iyyun siyasa su mutunta hukuncin kotu, ko da kuwa ba su gamsu da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ministan sufurin jiragen sama da bunƙasa sararin samaniya na Najeriya, Festus Keyamo, ya kuma yin magana game da Atiku Abubakar.

Festus Keyamo ya bayyana cewa babu wata babbar masifa da za ta afku a Najeriya idan aka hana tsohon mataimakin shugaban ƙasar yin takara.

Atiku
Atiku Abubakar mai neman mulkin Najeriya yana sallah a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Festus Keyamo ya sake maganar Atiku Abubakar

Ministan harkokin jiragen saman ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) a ranar Juma'a, 6 ga watan Nuwamba 2026.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotu: Adawa ta kara ƙarfi, jam'iyyun siyasa 9 sun goyi bayan ADC da Atiku

Festus Keyemo yana mayar da martani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Hukuncin kotun ya kuma soke halaccin shugabancin jam'iyyar da David Mark ke jagoranta. Wannan hukunci dai ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Najeriya.

Keyamo ya soki yadda 'yan adawa ke kallon kotu

Keyamo ya yi tambaya kan abin da ya kira rashin daidaito a yadda jam'iyyun adawa suke kallon hukuncin kotuna a cikin shekarun bayan nan.

Tsohon lauyan ya ce ya kamata 'yan siyasa su mutunta hukuncin kotu, ko da kuwa hukuncin ya yi daidai da muradunsu ko kuma ya ci karo da su.

Ya tuna da hukuncin Kotun Ƙoli da ya soke nasarar 'yan takarar jam'iyyar APC a Jihar Zamfara, tun daga gwamna har zuwa 'yan majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC

A lokacin, an ayyana 'yan takarar PDP a matsayin waɗanda suka yi nasara a shekarar 2019.

A wancan lokacin, Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2019, ya yi maraba da hukuncin kotun Allah ya isan.

An tuna masa yadda aka ji shi yana mai cewa nasara ce ga bin doka da tsarin zabe a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya ce:

“Babu wani abu da ya fi daɗin ji a kunnen muminai kamar ganin an yi adalci a cikin watan Ramadan mai alfarma.”

An kuma kawo misalin zaɓen Bayelsa

Keyamo ya kuma tuna da hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 13 ga Fabrairu, 2020, wanda ya soke nasarar David Lyon, ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Bayelsa.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Wannan hukunci ya ba ɗan takarar PDP, Douye Diri, damar zama gwamnan jihar duk da bai ci zaɓe ba.

Ministan ya ce a wancan lokacin APC ta amince da hukuncin kotun ba tare da kai wa ɓangaren shari'a hari ba duk da tana kallo ta rasa samun gwamna.

Ya ce saboda haka jam'iyyun adawa ma bai kamata su riƙa sukar alƙalai ko zargin kotuna a duk lokacin da aka yanke hukuncin da bai yi musu daɗi ba.

Keyamo ya ce:

“Ba za ku riƙa cin mutuncin alƙalai da kuma yi wa ɓangaren shari'a barazana ba kawai saboda hukunci bai zo muku yadda kuke so ba.”

Ya ƙara da cewa:

“Sama da kasa ba za su hade ba idan wani mutum mai suna Atiku Abubakar bai kasance cikin waɗanda za su tsaya takara a zaɓen 2027 ba.”

Abin da kotu ta yanke kan ADC da Atiku

A hukuncin da aka yanke ranar Alhamis, Mai shari'a Peter Lifu ya bayyana cewa kwamitin riƙon ƙwarya da David Mark ke jagoranta bai halatta ba.

Kara karanta wannan

2027: Sarkin Musulmi ya gana da Atiku da manyan ADC a Sokoto

Kotun mai zama a Abuja ta kuma amince da matsayin Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa daga Arewa maso Gabas.

Alƙalin ya soke matakan da kwamitin riƙon ƙwaryar ya ɗauka, ciki har da tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng