2027: Wike Ya Yi Damara, zai Gwabza da Shugaban Gwamnonin APC
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan burin Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, na zama Shugaban Majalisar Dattawa bayan zaɓen 2027 ba
- Wike ya yi wannan magana ne yayin da rashin jituwarsa da Uzodimma da wasu gwamnonin APC ke ƙara tsananta kan siyasar Najeriya
- Ya ce adawarsa da Uzodimma ta samo asali ne daga yadda yake ganin wasu gwamnonin APC na ƙoƙarin shafar zaɓen shugabannin Majalisar Ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai taɓa goyon bayan Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba bayan zaɓen 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takun saka tsakanin gwamnonin APC da Wike kan zaben shekarar 2027 da wasu abubuwa.

Source: Twitter
Wike ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da shirin Journalists’ Hangout na TVC, a daidai lokacin da rashin jituwarsa da Uzodimma da wasu gwamnonin APC ke ƙara bayyana.
Wike na adawa da Uzodimma
Wike ya ce wasu gwamnonin APC na ƙoƙarin yin amfani da zaɓen fitar da gwanin jam’iyyar wajen zaɓar ’yan Majalisar Dattawa da na Wakilai da za su iya rinjayar wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattawa ko Shugaban Majalisar Wakilai.
Ministan ya ce hakan na daga cikin dalilan da suka sa wasu gwamnonin APC ke adawa da shirin Rainbow Coalition da yake jagoranta.
Wike ya zargi Uzodimma
Wike ya zargi Uzodimma, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, da neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa bayan ya kammala wa’adinsa na gwamna.
Ya ce wasu ’yan siyasar da suka gaza samun tikitin APC a zaɓen fitar da gwani na iya neman wasu hanyoyin shiga takarar 2027.
A cewar Wike, hakan na iya haifar da samun ’yan majalisa da ba sa ƙarƙashin ikon gwamnonin jam'iyyar APC a sabuwar majalisar da za a kafa.
Magana kan Rainbow Coalition
Ministan ya jaddada cewa Rainbow Coalition ba wata hanya ce ta yi wa APC zagon ƙasa ba, yana mai cewa babban burinsa shi ne tallafa wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a sake zaɓensa a 2027.
Punch ta rahoto ya ce mambobin ƙawancen ya kamata su kasance masu ’yancin tallafa wa Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da suke zaɓar ’yan takarar da suke so a sauran matakan zaɓe.

Source: Facebook
Wike ya magantu kan Atiku
A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda gwamnonin G-5 suka tsara wata dabara da ta taimaka wa Peter Obi samun nasara kan Atiku Abubakar a wasu jihohin Kudu a 2023.
Wike ya ce G-5 ta lura da ƙarfin PDP da Atiku a yankin, sannan ta yanke shawarar barin Obi ya samu ƙuri’u a wasu jihohi domin hana Atiku cin gajiyar ƙarfin PDP a yankin.
Ya ce ƙungiyar ta yi irin wannan dabara a Edo da Cross River, amma ta hana Obi samun nasara a Rivers saboda abin da ya bayyana a matsayin illar siyasar da irin wannan nasara za ta iya haifarwa.
Asali: Legit.ng

