An Yi Babban Rashi a Najeriya, Bola Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Sanata

An Yi Babban Rashi a Najeriya, Bola Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Sanata

  • Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sanata kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos
  • Sanatar mai shekaru 56 ta rasu ne a Lagos bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya jefa iyalanta da abokan siyasarta cikin alhini
  • Tinubu ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga Lagos da Najeriya, inda ya yaba da gudummawar da ta bayar a harkokin gwamnati da ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - An tabbatar da rasuwar tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos wacce ta bar duniya a yau Asabar.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Sanata Idiat Oluranti Adebule da ta rasu bayan rashin lafiya.

Sanata Idiat ta riga mu gidan gaskiya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da marigayiya, Idiat Oluranti Adebule. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a yau Asabar 28 ga watan Nuwambar 2026.

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan bikin cika shekaru 56, Allah ya yi wa sanatar APC rasuwa

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos kafin rasuwarta ta wakilci mazabar Lagos ta Yamma a Majalisar Dattawa.

Adebule mai shekaru 56 ta rasu ne a Lagos bayan fama da gajeriyar rashin lafiya jim kadan bayan kai ta asibiti.

Tinubu ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga jihar Lagos, Majalisar Ƙasa da Najeriya baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya ce rasuwarta ta zo ne a lokacin da ake buƙatar ƙwarewarta da gudummawarta wajen hidimar al'umma.

Tinubu ya tuna da tarihin hidimar da marigayiyar ta yi wa al'umma, musamman lokacin da take riƙe da muƙamin mataimakiyar gwamnan Lagos.

Ya bayyana cewa rayuwarta a siyasa ta nuna jajircewarta na tsawon shekaru wajen gudanar da harkokin gwamnati, bunƙasa ilimi da ƙarfafa mata da matasa.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya yaba da gudummawar da ta bayar a ayyukan majalisa, yana mai cewa ta nuna ƙwazo wajen kare dimokuraɗiyya da wakiltar al'ummar mazabarta.

Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayiyar, gwamnatin jihar Lagos, abokan siyasarta, mambobin jam'iyyar APC, Majalisar Ƙasa da sauran waɗanda rasuwarta ta shafa.

Kara karanta wannan

Bayan tara malamai 2000, Barau Jibrin ya haɗa kan sarakuna 3000 saboda Tinubu da Abba

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya ba ta Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalanta da abokan hulɗarta ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Ƙarin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.