Bayan Abin da Ya Faru, Jami'ar Kano Ta Haramta Wa Dalibai bad da Kyaututtuka ga Malamai

Bayan Abin da Ya Faru, Jami'ar Kano Ta Haramta Wa Dalibai bad da Kyaututtuka ga Malamai

  • Jami’ar Northwest da ke Kano ta hana ɗalibai bai wa malamai kyaututtuka dangane da ayyukan jami’ar
  • Jami’ar ta bayyana cewa yin hakan cin hanci da rashawa ne da kuma babban laifi, tare da gargaɗin ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda ya karya dokar
  • Hukumar jami’ar ta ce dokar ta shafi ma’aikata da ɗalibai, ba tare da la’akari da manufar bayar da kyautar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jami’ar Northwest da ke Kano ta haramta wa ɗalibai da malamai bayarwa ko karɓar kyaututtuka a tsakaninsu dangane da ayyukan jami’ar.

Jami'ar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya umarnin zai fuskanci matakin ladabtarwa.

Kano.
Babbar kofar shiga jami'ar Northwest da ke cikin birnin Kano Hoto: Attahir Mahmud
Source: Facebook

Jami'ar Northwest ta kafa doka kan dalibai

Vanguard ta rahoto cewa jami’ar ta ayyana wannan dabi’a a matsayin cin hanci da rashawa da kuma babban laifi, inda ta jaddada cewa dokar ta shafi ma’aikata da ɗalibai, ko da kuwa manufar bayar da kyautar ta kasance mai kyau.

Kara karanta wannan

"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

Rijistaran jami’ar Northwest, Isyaku Adamu, ne ya sanar da wannan umarni a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Matakin ya biyo bayan rahotannin kyaututtukan da ɗalibai suka bai wa malaman da aka karrama a matsayin mafi nagartattu a rukuninsu, sun jawo hankalin jama’a.

Dalilin daukar wannan mataki

A cewar sanarwar, irin wannan dabi’a na iya bata sunan jami’ar tare da saɓa wa tanade-tanaden dokokin aiki da ƙa’idojin jami’ar na shekarar 2025, kamar yadda aka yi wa gyara.

Jami’ar Northwest ta bayyana bayarwa da karɓar kyaututtuka a matsayin ayyukan cin hanci da rashawa, da kuma halayen da za su iya jawo mata zubar da mutunci.

Adamu ya ce:

"Saboda haka, duk wani ma’aikaci ko ɗalibi da aka samu yana bayarwa ko karɓar kyaututtuka sakamakon ayyukan jami’a da aka yi masa, za a tuhume shi da aikata babban laifi, sannan jami’ar za ta dauki matakin ladabtarwa nan take bisa ƙa’idojinta.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Ya ƙara da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci bisa sashe na 16 na dokokin jami’ar.

Jami'ar Northwest ta yi jan hanakli

Saboda haka, Adamu ya buƙaci al’ummar jami’ar su kiyaye dokokinta, ƙa’idojin ɗabi’a da ingantattun hanyoyin gudanar da aiki domin guje wa matakin ladabtarwa.

Haka kuma, ya yi kira ga ma’aikata da ɗalibai su ɗauki umarnin da muhimmanci, inda ya ƙara da cewa: “Gyara tun wuri ya fi maganin nadama!”

Jami'a.
Babban allon sanarwa a kofar shiga jami'ar Northwest da ke jihar Kano Hoto: Attahir Mahmud
Source: Facebook

Jami’ar Northwest da ke Kano jami’a ce mallakar gwamnatin jihar Kano, wadda aka kafa a shekarar 2012.

An sauya mata suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule a shekarar 2017, kafin daga bisani ta koma amfani da sunanta na asali a shekarar 2024, bayan gyara dokar jihar da ta kafa jami’ar.

BUK ta hana shagalin Sign-Out

Kun ji cewa Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta haramta wa ɗaliban da suka kammala karatu yin bikin bankwana a harabar makaranta, wanda aka fi sani da Sign Out.

Jami’ar ta kuma ce an haramta amfani da rigunan yaye dalibai ko wasu tufafi na musamman da ɗaliban da suka kammala karatu ke yi domin ɗaukar hotuna ko gudanar da bukukuwan da jami’a ba ta amince da su ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262