"Dan Takarar Hadakar Adawa Zai Iya Kayar da Tinubu a Zaben Shugaban Kasa na 2027"

"Dan Takarar Hadakar Adawa Zai Iya Kayar da Tinubu a Zaben Shugaban Kasa na 2027"

  • Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi hasashen cewa ɗan takarar haɗakar jam’iyyun adawa zai doke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Tsohon mai ba Shugaba Tinubu shawara ya zargi gwamnatinsa da tabarbarewar tsaro, ƙara talauci da rarrabuwar kan ’yan Najeriya
  • Ya ce haɗakar na shirya babban taro domin bayyana shirinta na aiki tare da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban PRP na kasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa ɗan takarar da haɗakar jam’iyyun adawa za ta tsayar zai yi nasara a babban zaɓen 2027, inda zai kayar da Shugaba mai ci, Bola Tinubu.

Hakeem, wanda a baya ya kasance mai ba Tinubu shawara, ya ce shugaban ƙasar na jagorantar gwamnatin da ta gaza matuƙa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gano yadda ake amfani da kafafon sada zumunta a haddasa rikici a Najeriya

Hakeem Baba Ahmed.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: UGC

Da yake magana a gidan talabijin na Channels tv, ya ce Tinubu ya jagoranci aiwatar da manufofin da suka jefa mutane da dama cikin matsanancin talauci, tare da ƙara rarraba kan ’yan Najeriya fiye da kowane lokaci.

Ya ce:

“Rabuwar kanmu ta karu, yanzu abubuwa sun yi wa mutane wuya matuƙa. Abin da kawai ake gani shi ne wannan wadaka da kuɗi, nuna iko da mutanen da ke da tasiri a tsakanin jama’a.”

Ya yi hasashen nasarar ’yan adawa

Da aka tambaye shi ko wani ɗan takarar jam’iyyun adawa zai iya kayar da Shugaba Tinubu, ya ce:

Baba-Ahmed ya ce:

“Ban san wanda zai yi nasara ba, amma ina ganin ɗan takarar haɗaka zai yi nasara. Wane ne zai zama ɗan takarar haɗakar? To, har yanzu ba mu sani ba. Muna cikin ƙoƙarin ganin mun fito da tsari da zai ba mu damar tsira, sannan mu san wanda babu wata matsalar shari’a ko wasu ƙalubale da ke kan sa.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan adawa, ya nuna ƙarfin da yake da shi a Arewacin Najeriya"

"Don haka, har yanzu muna da sauran aiki kafin mu kai ga wannan mataki. Abin da muke yi a yanzu shi ne gina haɗakar ta yadda batun wanda za a mara wa baya daga ƙarshe ba zai zama matsala ba."

Zargin Shugaba Tinubu da gazawa

Hakeem Baba-Ahmed ya ce shugaban ƙasar ya nuna gazawa wajen gyara Najeriya, amma ya bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takarar haɗakar zai iya magance matsalolin ƙasar.

Ya ƙara da cewa na kusa da shugaban ƙasar sun amince cewa sauye-sauyen da gwamnatinsu ta aiwatar sun ƙara tsananta rayuwar ’yan Najeriya, yayin da suke neman ƙuri’u a wajen jama’a.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

A cewarsa, hakan ya nuna cewa ba za a iya amincewa da su su ci gaba da mulki na wasu shekaru huɗu ba.

Ya ce yawancin mutanen da ke yaƙin neman zaɓen Tinubu ba za su iya komawa yankunansu ba, waɗanda ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka suka mamaye, inda manoma suka shiga hannun ’yan ta’adda.

Baba-Ahmed ya zargi na kusa da Tinubu

Kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi wasu na kusa da Shugaba Bola Tinubu da ba shi bayanan ƙarya kan goyon bayan jama'a.

Ya ce wasu na jikin Tinubu na iya sa shi ya ɗauka cewa yana da farin jini sosai, ta hanyar dogaro da tabbacin gwamnoni da masu biyayya ga jam’iyya maimakon sauraron ra’ayoyin talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262