Kwamitin Sulhun APC Ya Fara Kokarin Sasanta Masari da Gwamna Radda

Kwamitin Sulhun APC Ya Fara Kokarin Sasanta Masari da Gwamna Radda

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tabbatar wa kwamitin sulhun APC na Arewa maso Yamma cewa zai yi aiki wajen tabbatar da hadin kan jam’iyyar a jiharsa
  • Radda ya kuma yi alkawarin hada kai da sauran shugabannin APC wajen ganin Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar sun samu gagarumar nasara
  • Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta zama iyali daya, don haka ya kamata mambobinta su hada kai wajen cimma manufofinsu a zaben 2027 da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tabbatar wa kwamitin sulhun jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma cewa zai tabbatar da hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar a jiharsa.

Radda ya bayyana hakan ne a daren Juma’a yayin ganawa da kwamitin a Abuja, inda ya jaddada muhimmancin hadin kai, fahimtar juna da daukar nauyin ci gaban jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Za ku dawo sayen fetur a N200 idan kuka zabe ni,' Dan takarar SDP

Dikko Radda da 'yan kwamitin APC
Kwamitin sulhun APC da Dikko Radda. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Hadiminsa, Ibrahim Kaulaha ya wallafa a Facebook cewa ya yi alkawarin hada karfi da karfe wajen neman goyon bayan jama’a ga Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaben 2027.

Radda zai hada kai da 'yan APC

Gwamnan ya ce APC ta zama iyali daya, don haka ya kamata mambobinta su hada kai domin karfafa jam’iyyar da cimma manufofinta.

A cewarsa, gwamnatin Katsina na kokarin karfafa jam’iyyar, kuma babu wani abu da zai sauya kudurinta na ci gaba da kasancewa cikin APC.

Radda ya ce:

"Kowa ya san irin aikin da muke yi a jihar Katsina. Mun tsaya daram kan APC, kuma mun san cewa iyali daya ne na siyasa. Don haka dole ne mu yi aiki tare, mu tsaya tare, mu kuma bi manufofinmu na bai daya a matsayin jam’iyya mai hadin kai."

Radda ya ce APC za ta yi nasara

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Mutumin Kwankwaso, Dantiye ya fadi wanda zai zaba a Kano

Radda ya tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa APC a Katsina a shirye take ta ba shi cikakken goyon baya domin sake zabensa a 2027.

Ya ce jam’iyyar za ta kara kokarin wayar da kan jama’a, karfafa rassanta da hada kan magoya bayanta domin samun nasara.

Gwamnan ya ce:

"Za mu yi iya kokarinmu wajen tabbatar da sake zaben Shugaba Tinubu. Nauyin da ke kanmu baki daya shi ne hada kan al’ummarmu, karfafa tsarin jam’iyyarmu da kuma yin aiki domin samun gagarumar nasara ga shugaban kasa da dukkan ’yan takarar APC a 2027."

Manyan APC sun halarci taron

Sanata Abu Ibrahim, daya daga cikin wadanda suka kafa APC kuma tsohon sanatan da ya wakilci Katsina ta Kudu, ne ya jagoranci kwamitin sulhun.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, da tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero.

Tsofaffin gwamnonin jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari da Barrista Ibrahim Shehu Shema, sun halarci taron tare da sauran mambobin kwamitin.

Radda ya ziyarci Daura

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya ce kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari ta karfafa zumuncinsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ka iya rasa muhimmiyar jiha a Arewa kan rigimar gwamna da manyan kasa

Radda ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai gidan Sardaunan Daura, Alhaji Auwalu Umar Faruq, tare da tawagar yakin neman zaben Tinubu–Dikko–Jobe.

Gwamnan ya kuma nemi addu’a da goyon bayan sarakunan gargajiya da al’ummar Daura ga ’yan takarar APC a zaben 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng