A Karshe dai Jam’iyyar APC Ta Fito da Makami Za Ta Yaki Nyesom Wike a Zaben 2027
- Shugaban APC ya ce jam’iyyarsu ba za ta goyi bayan ’yan takarar wasu jam’iyyun adawa ba a zaben 2027
- Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa gwamnonin APC za su yi wa ’yan takarar jam’iyyar kamfen a jihohinsu
- Wannan matsaya ta zo ne yayin da ake ce-ce-ku-ce kan shirin hadin gwiwar ‘Rainbow Coalition’ ta Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ba za su goyi bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu ba.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya nesanta APC da hadin guiwar siyasa na Rainbow Coalition da ke tare da tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Source: Getty Images
Shugaban APC ya nesanta jam'iyya da Rainbow Coalition
Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Shugaban APC na kasa ya ce gwamnonin jam’iyyar za su goyi bayan ’yan takararsu ne a dukkan matakan zabe na shekarar 2027.
Ya ce matsayin jam’iyyar a bayyane yake, kuma ba za ta goyi bayan duk wani dan takara da ba ya karkashin inuwar APC mai-ci ba.
Gwamnonin jam'iyya za su tallata APC a jihohinsu
Shugaban jam’iyyar ya kara da cewa gwamnonin APC za su yi wa ’yan takararsu kamfen a jihohinsu maimakon tallata wasu dabam.
Rahoto daga Tribune Online ya ce wannan matsaya ta zo ne a daidai lokacin da ake samun sabani da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ministan Babban Birnin Tarayya wanda dan jam’iyyar PDP ne yana rigima da gwamnonin APC kan gamayyar Rainbow Coalition.
Duk da yana tare da Bola Tinubu a sama, Wike yana yakar gwamnonin APC a wasu jihohi.
Shugaban APC ya fayyace matsayin jam'iyya
Wannan karo, Farfesa Yilwatda ya sanar da duniya cewa babu abin da ya hada jam’iyyar APC da hadin gambizar Rainbow Coalition.
A cikin wancan tafiya ta hadin gambiza, akwai masu neman zama gwamnoni a wasu jam’iyyun da suke taya Tinubu yakin neman zabe.
Da aka tambayi Yilwatda ko APC ta amince da Rainbow Coalition, ya bambanta matsayin jam’iyyar da zabin wasu daidaikun ’yan siyasa.
Ya jaddada cewa APC za ta fifita muradun jam’iyyarta a zabe, tare da tabbatar da cewa gwamnoninta za su yi wa ’yan takaransu kamfe.
A karshe, Yilwatda wanda yake jagorantar APC NWC ya karyata duk wani ra’ayi da ke nuna cewa matsayin jam’iyyar tasu bai fito fili ba.
Farfesan yana mai cewa jam’iyyar za ta goyi bayan ’yan takararta a dukkan matakan zaben 2027.

Source: TikTok
Nyesom Wike yana so a hukunta Rotimi Amaechi
An ji labari cewa Nyesom Wike yana so hukumar INEC ta ladabtar da Rotimi Amaechi da yake takarar mataimakin shugaban kasa a ADC
‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar ya fito ya ce babu mai zaben Bola Tinubu sai mahaukaci da kuma barayi, wannan ya fusata wasu.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Rivers ya yi barazanar hana Amaechi kamfe a mahaifarsa saboda cin mutuncin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng

