Gwamna Ya Jibga Mutane 3000 a Kwamitin Yakin Zabe don Nasarar Tinubu da APC
- Ahmadu Umaru Fintiri, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC mai mutum 3,000 a Adamwa
- Ya buƙaci mambobin kwamitin su haɗa kai wajen neman goyon bayan jama’a domin APC ta yi nasara a jihar
- A yayin taron da Gwamnan Adamawa ya jagoranta, wasu ’yan ADC da LP sun sauya sheƙa zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar APC.
APC ta kafa kwamitin kamfe mai mambobi sama da 3,000, inda ya buƙace su da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma.

Source: Facebook
Kwamitin yakin zaben jam'iyyar APC a Adamawa
Daily Trust ta ce gwamna ya dage domin ganin jam’iyyar ta yi nasara a zaɓen shugaban kasa, gwamna da ‘yan majalisa a 2027.
An gudanar da bikin ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Yola.

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano
Shugabannin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki daga sassan jihar suka halarta.
APC ta sa mutane 3000 a kwamitin kamfe
Fintiri ya bayyana cewa yadda aka haɗa kwamitin ya nuna an yi la’akari da bambancin al’adu, gogewa da kuma wakilcin jama’a.
Ya gargaɗi mambobin kwamitin da su guji duk wani abin da zai kawo cikas ga nasarar jam’iyyar, musamman cin amanar APC.
Gwamnan ya buƙace su da su mai da hankali wajen neman goyon bayan jama’a daga unguwanni zuwa ƙananan hukumomi.
Ɗan takarar gwamna, shugaban kwamitin sun yi magana
Ɗan takarar gwamnan jihar na APC, Alhaji Ahmed Galadima Aminu, ya yaba wa Fintiri bisa yadda ya jawo kowa cikin kwamitin.
Ahmed Galadima ya bayyana matakin a matsayin alamar shugabanci nagari, tare da alƙawarin cigaba daga inda Fintiri ya tsaya.
Shi ma daya daga cikin shugaban kwamitin Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya gode wa gwamnan da ya amince da shi.
Buba Marwa ya buƙaci mambobin kwamitin su tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna domin a samun nasara.

Source: Facebook
APC ta karbi 'yan adawa a Adamawa
Shugaban APC na jihar, Alhaji Hamza Bello Madagali, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda jama’a suka fito domin halartar taron.
People Gazette ta rahoto shi yana mai cewa hakan ya nuna haɗin kan jam’iyyar APC a Adamawa.
Ganin ba za a iya saka duk masu ruwa da tsaki a cikin kwamitin ba, don haka ya roki wadanda aka manta da su da su yi hakuri.
A wajen taron, an karbi wasu ‘yan adawa daga LP da ADC da suka shigo jirgin jam’iyyar APC mai-ci.
Mataimakin shugaban APC na kasa (Arewa maso gabas), Idris Shuaibu, ya karbi masu sauya-shekar, ya damka su ga Madagali.
A zabi APC in ji shugaba a Izala
An ji cewa Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya shawarci mabiyansa da dukkan al'ummar jihar Taraba da su goyi bayan jam'iyyar APC a 2027.
Ya bayyana cewa zaɓen jam'iyyar zai zama mafita da kuma kariya daga halin matsin siyasa da suka shafe shekaru 20 suna fuskanta a jihar.
Malamin ya kuma yi gargadi kan cewa goyon bayan wasu jam'iyyu ka iya maido da matsalolin da aka jima ana ta faman fuskanta a baya.
Asali: Legit.ng
