'Ya Koyar da Ni a Makaranta': Patience Ta Faɗi yadda Ta Haɗu da Jonathan Kafin Aure
- Patience Jonathan ta bayyana yadda ta fara soyayya da Goodluck Jonathan, inda ta bayyana cewa ya koya mata darasin Biology
- Tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Patience Jonathan, ta bayyana cewa mijinta, Goodluck Jonathan, shi ne malamin da ya koya mata darasin Biology
- Patience ta ce ta taba sana’ar sayar da ice cream, inda tsohon shugaban kasar ya rika taimaka mata wajen sayarwa da kuma kula da kayayyakin sana’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Tsohuwar uwargidan shugaban Najeriya, Patience Jonathan, ta bayyana yadda ta hadu da Goodluck Jonathan suka fara soyayya.
Ta ce alakarta da mijinta, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta fara tun suna matasa, inda ta ce ya taba zama malamin da ya koya mata darasin Biology.

Source: Getty Images
Matar Jonathan ta tuna haduwarsu
Patience ta bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), inda ta tuna yadda suka hadu da mijinta da kuma irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarta tun kafin su yi aure.
Ta ce:
“Na hadu da shi ne a cikin aji. Shi ne malamaina, ya koya min Biology. Ni da mijina ba mu dade muna soyayya ba saboda shi matashi ne, ni ma haka. Na taba sayar da ice cream, mijina yana taimaka min wajen sayar da shi. Ku tambayi duk wanda ya sani. Muna da babban shago da firji.
“Mun sayi firji, muna hadawa da sarrafa ice cream. Muna da kekuna da mutanen da ke zuwa karbar kayan domin su je su sayar. Da safe za su zo su kwashe ice cream din domin sayarwa. Ni kuma nakan je makarantu ina sayarwa, daga nan in dawo gida, mijina ya taimaka min wajen tsaftace firjin. Muna yin komai tare.”

Source: UGC
Ta yi magana kan zargin juya Jonathan
Ta kuma musanta zargin cewa tana juya mijinta ko kuma tana da ikon sarrafa shi a lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasa da bayan barinsa.
Ta ce mutane na yawan cewa tana juya mijinta, amma ta tambayi yadda mace za ta iya mallakar ikon sarrafa namiji.
Haka kuma, Patience ta bayyana cewa tana sane da matakin da mijinta ya dauka na amincewa da shan kayen da ya yi a zaben shugaban kasa na 2015, inda ya taya marigayi Muhammadu Buhari murnar lashe zaben.
Ta ce tana cikin wadanda suka san da matakin da mijinta ya dauka, kuma ta ji dadin hakan saboda tana son su bar mulki cikin aminci.
Ta ce:
“Babu wani abu da mijina yake yi wanda ba na tare da shi. Ina da masaniya kan hakan. Na yi farin ciki. Ina son mu bar mulki, saboda ba na son a kashe mijina.”
Patience Jonathan ta magantu kan kishiyarta
Mun ba ku labarin cewa Patience Jonathan ta yi magana kan zargin auren Goodluck Jonathan da wata mata, inda ta tambayi ko doka ta amince da auren mace biyu a kotu.
Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa ta yi tambayar ne yayin wata hira da aka yi da ita bayan an tambaye ta game da Ayima Lott-Jonathan.
Kalaman nata sun zo ne kwanaki bayan Ayima ta ƙaddamar da littafinta mai suna Gold Dust: Treasures of Quiet Years a Abuja.
Asali: Legit.ng

