Tinubu Ya Kawo Jerin Ayyukan da Yake Yi a Arewa Ana Shirin Shiga Kamfen Kaduna
- Bayo Onanuga ya jero wasu daga cikin ayyukan da Bola Ahmed Tinubu ya kawo Arewa maso yamas
- Hadimin shugaban kasar ya bada misali da tituna a Kaduna, Sokoto, Kano da ake yi ko kuma aka gama
- Onanuga ya ce ayyukan jirgin kasa a Kaduna da Kano, za su ci dala miliyan 865 da Naira tiriliyan 1
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Bayo Onanuga ya jero ayyukan hanyoyi da gwamnatin Bola Tinubu ta ke yi ko ta kammala a jihohin Arewacin Najeriya.
Hadimin shugaban kasar ya yi wannan ne ganin cewa ranar Asabar Bola Tinubu zai fara fita yawo yakin neman zaben 2027.

Source: Facebook
Gwamnatin Bola Tinubu ta haska hanyar Abuja
Kamar yadda ya bayyana a shafin Facebook, ya ce an kammala shimfida fitilun titi a hanyar Abuja–Kaduna na tsawon kilomita 81.

Kara karanta wannan
Raddin da Jalo Jalingo ya yi wa sarakuna ya sa ya ji babu daɗi hannun ƴan Facebook
Ya tabbatar da cewa an shirin kaddamar da aikin a yau, ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.
Ya ce masu tafiya da mota zuwa Kaduna daga birnin tarayya na Abuja za su ga an haska titin ban da shararrar hanya da aka yi.
Ayyukan titi a jihohin Arewa maso yamma
Bayo Onanuga yake cewa ana gudanar da ayyukan tituna masu tsawon kilomita 4,084 a yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Cikin manyan titunan akwai hanyar Sokoto–Zamfara–Zariya da kuma hanyar Kano–Kongolam.
Cikin ayyukan da Gwamnatin tarayya ta gada ko wadanda aka kirkira, an kammala titunan da sun kusa kai kilomita 350 zuwa yanzu.
A sahun nan akwai kilomita 81 da wani kilomita 164 da aka ci a hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano da aka dade ana ta ginawa.
Na biyu shi ne titin kilomita 77 na Kaduna–Pambeguwa da za a kaddamar a lokacin da shugaban kasa ya je kamfe a jihar Filato.
Wasu ayyukan da ake kan yi a yau
Ayyukan da yanzu ake tsakiyar su kuwa sun hada da babban titin Sokoto–Badagry.
Haka zalika akwai katafaren aikin da ake yi na fadada titin Sokoto–Zamfara–Zaria wanda yanzu Onanuga ya ce an yi kusan rabi.
Akwai titunan Kano–Kongolam, Zaria–Hunkuyi da kuma na Mando–Birni Gwari wadanda gaba dayan su sun zarce kilomita 400.
Tinubu ya dauko ayyukan jirgin kasa
A bangaren jirgin kasa, akwai aikin jirgin Kano da zai ci kudi da kuma jirgin kasa da za yi a cikin birnin Kaduna a kan $865m.
Hadimin shugaban kasar ya ce kudin aikin dogon Kano ya haura Naira tiriliyan daya.
Tsohon gwamnan Neja ya ce sai Tinubu
Ana da labari Mu’azu Babangida Aliyu wanda shi ne sakataren PDP-BOT yana yi wa APC aiki a zaben shugaban kasa.
Sannan tsohon gwamnan ya kafa kungiyar ‘Bago Actualization Group for New Niger’ a jihar Neja da ke tallar gwamna mai-ci.
A matakin kasa, Babangida Aliyu ya lallaba yana tallata tazarcen Bola Tinubu da jam’iyyar APC duk da ba a ji ya bar PDP ba.
Asali: Legit.ng
