Tsohon Gwamna kuma Shugaba a PDP Ya Tsumbula Kafa a APC Babu Wanda Ya Ji Labari
- Dr Mu’azu Babangida Aliyu yana tare da jam’iyyar APC a zaben 2027 alhali an san shi 'dan adawa ne a PDP
- Tsohon gwamnan Nejan yana goyon bayan Umaru Bago ya zarce kuma har ya kafa kungiyar tallar shi a jiharsa
- Shugabannin APC da wani hadimin shgaban kasa sun tabbatar da cewa ‘dan siyasar ya zama nasu a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Alamu suna nuna cewa Mu’azu Babangida Aliyu ya yi sabon gida a siyasa bayan tsawon shekaru yana jam’iyyar PDP.
Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya yi shekaru takwas daga 2007 zuwa 2015 matsayin gwamnan jihar Neja a lokacin PDP tana mulki.

Source: Facebook
2027: Muazu Babangida Aliyu ya jefa kafa a APC?
Legit Hausa ta fahimci cewa watakila dai Mu’azu Babangida Aliyu ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC mai-ci a yanzu.
Hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada ya fara kyankyasa wa duniya wannan labari a dandalin X a ranar 17 ga watan Oktoba 2026.
Abin da ya fi jan hankali shi ne mafi yawan mutane ba su samu labarin sauyin ba duk da kuwa lokaci ne da ake cikin yakin neman zabe.
Muazu Babangida yana cikin PDP-BOT
Kafin janye kafarsa, Mu’azu Babangida Aliyu yana cikin ‘yan majalisar amintattu (BOT) a matakin kasa na jam’iyyar PDP mai adawa.
Jaridar Daily Post ta rahoto lokacin da majalisar BOT ta nada shi a matsayin sakatarenta a Najeriya.
Shugaban BOT, Sanata Adolphus Wabara ya ce sun dauki matakin ne domin karfafa jam’iyyar bayan hukuncin kotun daukaka kara.
Tsohon gwamnan yana yi wa APC kamfe
Watanni bakwai da wannan nadi sai aka ji cewa Talban Minna yana tallar 'yan takaran APC duk da a baya ya karyata cewa zai sauya-sheka.
Babu mamaki rikicin cikin gidan da ya barka jam’iyyar hamayyar ta sa ya yi ban-kwana da ita, ya kama layin APC domin a dama da shi.
A lokacin da aka dage da yakin neman zabe sai aka ji cewa tsohon gwamnan yana goyon bayan Gwamna Umaru Mohammed Bago.
The Sun ta ke cewa Babangida Aliyu ya kafa wata kungiyar hadin gwiwar ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.
Kungiyar Bago Actualization Group for New Niger za ta wayar da kan jama’a tare da neman goyon bayansu domin Bago ya zarce.
Talban Minna ya kaddamar da kungiyar a gidansa da ke Abuja ranar 12 ga Oktoba 2026.
Ya ce kungiyar ba ta takaita ga wata jam’iyya guda ba, domin tana kunshe da ’yan PDP, APC, ADC, NNPP da sauran jam’iyyu.
Tsohon gwamnan ya buƙaci mambobin kungiyar su kasance masu gaskiya, ladabi da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata su fifita ci gaban Neja da walwalar al’ummarta fiye da muradun kansu da bambancin siyasa.
Har zuwa lokacin Dr. Babangida Aliyu bai sanar da duniya cewa ya bar PDP ba, ya dai zo da hadin gambiza irin na Nyesom Wike.
Tsohon gwamnan Neja ya shigo APC - Hadimin Tinubu

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023
Ban da Bago Actualization Group for New Niger, Olusegun Dada ya bayyana cewa yanzu sakataren na PDP-BOT yana tare da su a APC.
Ya rubuta:
"Tsohon gwamna Muazu Babangida Aliyu yana tare da APC daBola Ahmed Tinubu yanzu 100%."
A nan ne mutane suka rika yi masa raddi cewa yanzu zamanin shi ya wuce, an daina maganar shi a siyasar Neja ko ta yankin Arewa.
A shafinsa na Facebook, an ga tsohon gwamnan ya cigaba da mu'amala da jam'iyyar PDP - yana tafiye-tafiye da su Kabiru Tanimu Turaki.
Sakataren APC ya tabbatar da dauke jagora a PDP
A hirarsa da tashar Channels, Sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru ya tabbatar da zancen nan da yake maganar karfin jam'yyarsu a Arewa.
Sanata Basiru ya ce:
“Har ma wasu daga cikin ’yan jam’iyyar adawa sun canza, ciki har da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu. Yanzu duk suna zuwa su shiga APC , su yi aiki da ita.
“Gaskiyar magana ita ce, a yau, idan ka dubi manyan jiga-jigan Arewacin Najeriya, za ka ga suna tare da mu. Haka kuma, talakawan Arewacin Najeriya suna tare da mu.”
'Yan adawa za su tsaida mutum 1 a 2027
Labarin da aka samu a baya shi ne 'Yan kungiyar G100 da gaske su ke yi wajen magance matsalar raba kan ‘yan adawa a zaben badi.
Gamayyar hamayyar ta kusa fito da ‘dan takaran da ake sa ran kowa zai bi bayan shi domin ya tunakari Bola Tinubu da jam'iyyar APC.
Ana so a fito da mutum guda tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da sauran masu neman mulki a PRP da wasu jam'iyyu.
Asali: Legit.ng


