Rikicin APC a Jihar Kano Ya Yi Kamari, An Aika Sakon Gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Rikicin APC a Jihar Kano Ya Yi Kamari, An Aika Sakon Gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

  • Jigon APC a Jihar Kano, Aminu Shehu Sharada, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da Sanata Abdulaziz Yari su shiga tsakani don yin sukhuba jam’iyyar
  • Ya yi gargaɗin cewa rikicin cikin gida na iya rage wa APC damar samun nasara a zaɓen 2027 idan ba a gaggauta shawo kansa ba
  • Sharada ya ce shugabannin jam’iyyar a Kano na buƙatar tattaunawa da sulhu domin gina haɗin kai kafin babban zaɓen ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Aminu Shehu Sharada, ya nuna damuwa kan rigingimun cikin gida.

Ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Abdulaziz Yari, su shiga tsakani donin warware rikice-rikicen cikin gida da suka raba kan mambobin APC a Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da bukatar da ka gabatar masa a wurin gangamin kamfe a jihar Kebbi

Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Sharada ya yi gargaɗin cewa saɓanin ra’ayi da ke tsakanin ’yan jam’iyyar na iya kawo cikas ga damar APC ta samun nasara a zaɓe mai zuwa idan ba a gaggauta magance matsalar ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An zargin APC na fama da rikici

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Alhamis, jigon APC ya ce waɗanda ke nuna cewa komai yana tafiya daidai a APC ta Kano ba sa isar wa Shugaban ƙasa sahihin bayanin halin da ake ciki.

Ya ce:

“Duk wanda ke nuna cewa komai yana tafiya daidai a APC ta Kano, ba ya bai wa Shugaban ƙasa cikakken bayanin halin da ake ciki.
"Akwai saɓani da damuwa a fili tsakanin shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki, kuma idan ba a magance su da wuri ba, za su iya haifar da babbar matsala ga jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Sharada ya ce babban nauyin da ke kan masu ruwa da tsaki a APC ta Kano a yanzu shi ne gina haɗaɗɗiyar jam’iyya da za ta iya samun nasara a dukkan matakan zaɓe.

Ya lissafa zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai da kuma ’yan Majalisar Dokokin Jiha a matsayin muhimman zaɓukan da ya kamata jam’iyyar ta yi aiki domin samun nasara a cikinsu.

A cewarsa, APC ta Kano tana da ɗimbin mambobi da masu ruwa da tsaki masu kishin jam’iyyar, amma tana buƙatar shugabanci da zai haɗa kowa wuri guda, ya saurari damuwarsu tare da samar da manufa guda.

Sharada ya ƙara da cewa ƙalubalen da ke fuskantar jam’iyyar sun fi muradun wasu mutane muhimmanci, inda ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki su warware saɓaninsu domin amfanin APC.

“Saboda haka ne nake yin kira cikin gaggawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Abdulaziz Yari, da su tsiga tsakani domin magance matsalar a Kano," in ji shi.

Sanatan Kano ya gargadi APC

Kun ji cewa Sanata Suleiman Kawu Sumaila ya ce wahalar rayuwa da ta biyo bayan gyare-gyaren tattalin arziƙin Tinubu ta fusata mutane a Arewacin Najeriya.

Dan Majalisar dattawan ya buƙaci APC ta sake kusantar talakawatare da nuna tausayi ga halin da suke ciki gabanin zaɓen 2027 idan tana son samun nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262