Zaben 2027: Yadda Tinubu, Atiku da Peter Obi ke Fafatawar Neman Nasara a Jihohin Arewa 5

Zaben 2027: Yadda Tinubu, Atiku da Peter Obi ke Fafatawar Neman Nasara a Jihohin Arewa 5

  • Wani sabon rahoto ya yi nazari kan yanayin siyasa a jihohi biyar masu muhimmanci gabanin zaben shugaban kasa na Najeriya na 2027
  • Sauya shekar Gwamna Ahmadu Fintiri zuwa APC da Gwamna Bala Mohammed zuwa APM ya sauya lissafin siyasa a Adamawa da Bauchi
  • Kano na da masu rajistar zabe kusan miliyan 5.9, yayin da APC ta ci gaba da dasa karfin siyasa a Kwara tun 2019, lamarin da ya sa jihohin suka zama muhimman wuraren sa ido gabanin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Shugaban sashen Hausa na Legit.ng, Salisu Ibrahim, yana da gogewar sama da shekaru shida wajen kawo rahotannin siyasa, zabe, harkokin jama'a da shugabanci a Najeriya da Afirka.

Jihar Kano — Wani sabon nazari da wata jaridar Najeriya ta gudanar ya duba yanayin siyasa a jihohi biyar da suka hada da Kano, Adamawa, Bauchi, Benue da Kwara, yayin da ake fara shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.

Rahoton da jaridar The Nation ta wallafa ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, ya yi nazari kan yadda tsarin jam'iyyu, sauya sheka da tasirin manyan 'yan siyasa za su iya shafar yadda masu zabe za su kada kuri'a a kowace jiha.

Kara karanta wannan

Hadimin Davido ya saba da shi kan Tinubu, ya fadi alherin mulkin dan Arewa

Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC da Peter Obi na jam'iyyar NDC na daga cikin manyan 'yan siyasar da ke shirin fafatawa a zaben.

Fafatawar APC, ADC da NDC a zaben 2027
Yadda za ta kaya a zaben 2027 | Hoto: @aonanuga1956, @atiku, @PeterObi
Source: Facebook

Kano, Adamawa da Bauchi

Kano, wadda ke da masu rajistar zabe kusan miliyan 5.9 a kananan hukumomi 44, na daga cikin jihohin da ake ganin za su taka muhimmiyar rawa a zaben.

Rahoton ya bayyana cewa alakar da ke tsakanin Tinubu, Obi da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, na iya tasiri wajen tantance yadda jihar za ta kada kuri'a.

A zaben 2023, Kwankwaso ya nuna karfin tsarin siyasar cikin gida ta hanyar sakamakon da ya samu karkashin jam'iyyar NNPP.

A Adamawa, Atiku ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u 417,611, yayin da Tinubu ya samu 182,881, bisa bayanan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Sai dai sauya shekar Atiku daga jam'iyyar PDP zuwa ADC ya sanya ake duba ko zai iya rike magoya bayansa duk da sauyin jam'iyya.

Sauya shekar Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zuwa APC tare da dubban magoya bayansa ya kara karfin jam'iyyar mai mulki a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 12 da Shugaba Tinubu zai iya zuwa kamfe kafin babban zaben 2027

Rahoton ya kuma bayyana tasirin Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, a matsayin wani abin lura a jihar.

Siyasar Bauchi da APC a baya da yau

A Bauchi ma, sauye-sauyen kawance sun sauya lissafin siyasa. Atiku ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a jihar da kuri'u 426,607, yayin da Tinubu ya samu 316,694.

Sai dai ficewar Gwamna Bala Mohammed daga PDP zuwa jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta kara dagula lissafin siyasar jihar.

Ana sa ran Mohammed zai mara wa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, baya, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na APM. Wannan ya haifar da tambayoyi kan makomar tsoffin magoya bayan Atiku a jihar.

A daya bangaren, APC na gina shirinta na yakin neman zabe bisa tasirin wasu manyan 'yan siyasa, ciki har da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Bala Mohammed ya kuma amince da rawar da Tinubu ya taka wajen magance matsalolin tsaro a jihar, inda ya ce:

"Lokacin da 'yan bindiga suka kusa mamaye mu, babu wanda ya zo ya taimaka mana. Na je wurinsa, kuma ya amsa bukatata duk da cewa ina jam'iyyar adawa."

Kara karanta wannan

Kwana 1 bayan ƙaddamar da kamfe, tsohon shugaban NPA ta ƙasa ya fice daga APC a Kano

Ya kara da cewa Tinubu ya amince da tura bataliyoyin sojoji biyu zuwa kananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa.

Benue da Kwara: Karfin jam'iyya

A jihar Benue, rahoton ya bayyana APC, PDP da ADC a matsayin manyan jam'iyyun da ya kamata a sanya wa ido, inda ya ce yadda za su iya hada kan magoya baya da gudanar da yakin neman zabe zai iya tasiri ga sakamakon zaben.

A Kwara kuwa, APC ta ci gaba da rike karfin siyasa tun bayan nasarar tafiyar O to Ge a shekarar 2019.

Jaridar ta bayyana cewa matakan da magoya bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, za su dauka, da kuma wadanda ba su gamsu da tafiyar APC ba, na iya shafar yadda kuri'u za su rarrabu a jihar.

Legit.ng ta ruwaito cewa wannan nazari ya dogara ne kan yanayin siyasar da ake ciki zuwa ranar 18 ga Oktoba, 2026, kuma ba ya tabbatar da sakamakon zaben da za a gudanar nan gaba.

Ga yadda rahoton ya bayyana hasashen siyasar jihohin biyar gabanin zaben shugaban kasa na 2027:

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

  1. Kano: Fafatawa tsakanin Tinubu da hadakar Obi da Kwankwaso.
  2. Adamawa: Ana sa ran Atiku da Tinubu za su yi gogayya mai zafi.
  3. Bauchi: Tinubu da Atiku na daga cikin manyan 'yan takarar da ake sa ido a kansu.
  4. Benue: APC ta Tinubu na da karfin siyasa a jihar.
  5. Kwara: Rahoton ya yi hasashen cewa APC za ta iya samun gagarumar nasara a zaben shugaban kasa a jihar.

Kwankwaso ga ADC kan batun zaben 2027

A wani labarin, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani mai zafi ga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kan zarge-zargenta.

Kwankwaso ya ce NDC ba za ta janye wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, takara domin goyon bayan jam’iyyar ADC ba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a shafin X yayin da yake mayar da martani kan zargin da ADC ke yi masu cewa suna yi wa APC aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng