An Yi wa Wasu Bayin Allah Rauni daga Zuwa Taron Yakin Zaben Jam’iyyar APC
- An samu arangama tsakanin matasan Ijaw da Itsekiri wajen kamfen APC a Warri sakamakon takaddamar sake fasalin rumfunan zaɓe
- Ƙungiyar matasan Ijaw ta yi zargin an raunata mutum takwas, yayin da wani wakilin ƙabilar Itsekiri ya ce an kai wa matasansu hari
- An nemi hukumomin jihar Delta su yi bincike tare da kira al'ummomin yankin su guji rikici domin tabbatar da zaman lafiya gabanin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Delta - Rikicin da ake ta samu kan batun sake fasalin rumfunan zaɓe a yankin Warri ya sake barkewa tsakanin Ijaw, Itsekiri da Urhobo.
Wannan lamari ya jawo an ji raunuka yayin wani gangamin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Delta a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba 2026.
Tashar talabijin TVC ta rahoto cewa rikicin dai ya samo asali ne daga rashin jituwa kan aikin sake fasalin rumfunan zaɓe da Hukumar INEC ta yi.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da wannan aiki ƙaramar hukumar Warri ta Kudu, abin da bai yi wa wasu matasa dadi ba.
An yi amfani da taron APC wajen tada rikici
Rigima ta barke tsakanin matasan Ijaw da Itsekiri yayin wani gangamin APC da aka gudanar a a makarantar Nana Model College da ke Warri.
Lamarin ya tayar da hankula a wajen taron, har ta kai wasu daga cikin magoya bayan APC ‘yan kabilar Ijaw sun yi basaja domin gudun a gane su.
Matasa maza da mata da ke sanye da rigunan kamfen ɗin ƙungiyar PBAT Door-to-Door, sun tube taguwoyinsu saboda tsoron a kawo masu hari.
Matasan Itsekiri sun nuna rashin amincewarsu da kasancewar ‘yan Ijaw a ƙaramar hukumar Warri ta Kudu, wannan ya ƙara rura wutar ƙabilun yankin.
Tun farko an nemi canza wurin gangamin APC
Wata majiya ta bayyana cewa tun ranar Litinin, matasan Ijaw suka buƙaci shugabannin APC na jihar Delta su sauya wurin gudanar da gangamin.
An nemi a fasa yin taron a makarantar, a tafi filin wasa na Mai martaba Tunde Smooth da ke NPA, saboda ana fargabar yiwuwar a auka wa mutane.
Haka kuma, labari ya zo a jaridar Leadership cewa wasu ƙungiyoyin matasan Itsekiri sun yi barazanar hana mutanen Ijaw halartar taron na APC.
Rahotanni sun nuna cewa wasu matasan Itsekiri sun gudanar da zanga-zanga saboda rashin amincewarsu da shigar da ‘yan Ijaw cikin rumfunansu.
'Yan Ijaw da Itsekiri suna maida wa juna martani
A yayin da rikicin ya ƙara tsananta, ɓangarorin biyu sun riƙa zargin juna har aka jawo tashin hankali.
Da yake magana a madadin ƙungiyar matasan Ijaw na reshen Ogbe-Ijoh, sakataren ƙungiyar, Douye Vincent, ya zargi matasan Itsekiri da tada fitina.
Kwamred Douye Vincent ya ce Itsekirawa suka kai wa magoya bayan Ijaw da suka halarci gangamin hari har mutane aƙalla takwas suka samu rauni.
Sai dai wani wakilin al'ummar Itsekiri, Prince Afotan Debi, ya musanta wannan zargi, shi ya bayyana cewa ‘yan Ijaw ne suka jawo wannan rikici.
Prince Debi ya zarge su da sanya rigunan da ke ɗauke da rubutun 'Ijaws in Warri South' kuma ya ce sai da aka kai wa wasu matasan Itsekiri farmaki.
Ana tunanin cewa an mutu a sanadiyyar harin

Kara karanta wannan
2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa
Wata babbar ƙungiya ta ƙabilar Ijawa Allah-wadai da harin, tana cewa mutane da dama sun samu raunuka, yayin da ake fargabar an kashe mutum ɗaya.
Ƙungiyar ta buƙaci jami'an tsaro su gudanar da bincike, gano waɗanda suka aikata laifin tare da hana yiwuwar ramuwar gayya yayin da ake ta kamfe.

Source: UGC
Manyan Arewa sun gagara shawo kan sabaninsu
An ji cewa sarakuna da wasu manya sun yi zama a gidan Sarkin Musulmi amma ba a iya kashe wutar rikicin shugabancin kungiyar dattawan Arewa ba.
Saɓanin ya shafi wa'adin wasu daga cikin shugabanni da zargin almundahana da kusan Naira biliyan 3.9 na gudummawar da aka ba wa ƙungiyar kwanaki.
An rufe sakatariyar ACF da ke Kaduna, yayin da shugabannin ɓangarorin biyu ke zargin juna da haddasa rikicin, yanzu har magana ta kai wajen gwamnati.
Asali: Legit.ng
