Ana Zargin ‘Dan Takaran Gwamnan ADC da Shiga Yarjejeniya a Asirce da Jam’iyyar APC
- ‘Dan takarar gwamnan Enugu na ADC, Obodoeze Ocho, ya musanta jita-jitar kulla yarjejeniya da jam’iyyar APC a asirce
- Ya yi alkawarin inganta tsaro, farfado da noma, samar da ayyukan yi da rage haraji kan masu karamin karfi idan aka zabe shi
- Cif Obodoeze Ocho ya kaddamar da manufofin da yake sa ran aiwatarwa daga 2027 zuwa 2031 muddin ADC ta kafa gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Enugu - ‘Dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a jihar Enugu, Obodoeze Ocho, ya musanta zargin cewa ya kulla wata yarjejeniya a boye da APC.
Da yake jawabi a taron manema labarai na farko da ya gudanar a Enugu ranar Alhamis, Ocho ya bayyana manufofinsa na sauya fasalin jihar Enugu.

Source: Twitter
Obodoeze Ocho ya fito da manufofinsa a ADC
Punch ta ce Obodoeze Ocho ya bayyana manufofinsa na gina sabon tsarin mulki nagari, tsaro mai inganci, da gwamnati mai gaskiya da rikon amana.

Kara karanta wannan
Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki
Ocho ya soki yadda gwamnatin Peter Mbah ke tafiyar da harkokin tsaro, yana mai cewa amfani da fasaha kadai bai magance matsalolin tsaron jihar ba.
Ya nemi jin inda jiragen sama marasa matuki da gwamnatin jihar ta saya domin yaki da rashin tsaro suke.
Duk da cewa ya yaba da kafa cibiyar kula da harkokin tsaro da sanya kyamarorin CCTV a hanya, ya ce an fi mayar da hankali ne kan babban birnin Enugu.
Yana zargin an bar kauyuka da sauran wurare suna fuskantar barazana saboda rashin isasshen kariya.
‘Dan takaran gwamnan ya ce idan aka zabe shi a ADC, zai kafa babbar cibiyar kula da tsaro wadda za ta hada da kyamarorin CCTV masu inganci a wurare.
Zai maida hankali a kan wurare irinsu Uzo-Uwani, Isi-Uzo, Aninri, Ezeagu da hanyar Ugwuogo.
Ya kuma yi alkawarin kafa kungiyoyin sa-kai na sa ido kan tsaro da rundunonin kai daukin gaggawa a dukkan kananan hukumomi 17 da ake da su a jihar Enugu.
Sauran alkawuran da 'dan takaran na ADC ya yi
Haka kuma, The Nation ta rahoto ya ce zai samar da tsarin inshora da walwalar jami'an tsaro.
Dangane da kashe manoma da ake zargin wasu makiyaya suna yi a Uzo-Uwani, Ocho ya ce a karkashin gwamnatinsa, babu wanda zai gaza zuwa gona.
‘Dan takaran ya ce noma na daga cikin manyan hanyoyin da za su iya samar da arziki a Enugu, amma ana kuka da rashin wuraren adana abin da aka noma.
Idan ADC ta kaga gwamnati, Ocho ya sha alwashin kafa bankin abinci da zai rika sayen amfanin gonar da manoman jihar suka samu domin gudun a yi asara.
Ya ce zai kafa cibiyoyin sarrafa rogo, doya, shinkafa da kayan lambu da nufin a maida su kayayyakin da za a iya sayarwa kuma don jama’a su samu ayyukan yi.
Ocho yana tare da ADC ne ko APC?
A wurin ne ya warware jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta, ya musanta cewa bai da wata alaka ko yarjejeniya da jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce wasu 'yan siyasa ne ke yada wannan labari saboda suna tsoron yadda yake samun karbuwa a jihar, yake tabbatarwa jama’a cewa yana tare da ADC.
Ocho ya kuma yi alkawarin farfado da ma'adinai da albarkatun jihar tare da yin alkawarin rage haraji da ya ce gwamnati mai-ci ta lafta wa talakawa a Enugu.
Ya ce an addabi mata da ke neman kai, direbobin Keke Napep, masu shaguna da kananan 'yan kasuwa.

Source: Twitter
Mai harin takarar shugaban kasa a LP ya shiga APC
Ɗan takarar shugaban kasa a tsagin jam’iyyar LP aka ji labari ya janye takararsa domin ya goyi bayan Bola Tinubu da APC a shekarar 2027.
Ya canza shawara ne danzu da ya shiga ƙungiyar City Boy Movement saboda alakar da ke tsakanin sa da yaron shugaban kasa wato Seyi Tinubu.
Kennedy Ahanotu ya koka game da yadda aka danne su a jam'iyyar ADC lokacin da aka karbi sababbin shiga duk da cewa sun dade ana yi da su.
Asali: Legit.ng

