Zaben 2027: Tinubu Ya Fadi Babban Abin da Atiku Ya Rasa

Zaben 2027: Tinubu Ya Fadi Babban Abin da Atiku Ya Rasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi zargin cewa babu wani daga cikin tsofaffin gwamnonin Adamawa biyar da ya yi mulki da ke goyon bayan Atiku
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Tinubu a gangamin yaƙin neman zaɓen APC da aka gudanar a Akure
  • Shugaban ƙasar ya kuma soki tarihin mulkin Peter Obi a Anambra, inda ya bayyana ayyukansa a matsayin babu komai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tambaya kan ƙarfin siyasar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, a jiharsa ta Adamawa.

Tinubu ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da goyon bayan manyan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar.

Tinubu ya ragargaji Atiku
Shugaba Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Akure, babban birnin Jihar Ondo, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Amaechi ya kira ruwa, Shettima ya taso shi a gaban kan taba kimar Buhari

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Tinubu a taron, inda ya isar da saƙon shugaban ƙasar ga magoya bayan jam’iyyar.

Tinubu ya kuma yi amfani da damar wajen sukar tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi.

Ya yi kira ga al'ummar Ondo su mara masa baya

A cikin saƙonsa, Tinubu ya bukaci al’ummar Jihar Ondo su goyi bayan gwamnatinsa tare da mara masa baya domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Ya tuna gangamin yaƙin neman zaɓen da APC ta gudanar a jihohin Kaduna, Cross River, Nasarawa, Ekiti, Akwa Ibom, Rivers da Ebonyi, inda ya bayyana tarukan a matsayin waɗanda suka yi nasara.

Shugaban ƙasar ya buƙaci al’ummar Ondo su nuna irin wannan goyon baya ga takararsa, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Da yake isar da saƙon Tinubu, Shettima ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

"Shugaban ƙasarmu ya umarce mu da mu yi magana a madadinsa.”

Me Tinubu ya ce Atiku bai da shi?

Tinubu ya karkata ga sukar Atiku, inda ya yi tambaya kan matsayin tsohon mataimakin shugaban ƙasar a siyasance a jiharsa ta Adamawa.

Ya yi ikirarin cewa babu wani daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar biyar da suka mulki Adamawa da ke goyon bayan Atiku.

A cewarsa, wannan na nuna cewa Atiku ba shi da goyon bayan manyan shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a jiharsa.

"Atiku Abubakar ɗan Jihar Adamawa ne. Daga cikin gwamnonin jihar biyar da suka yi mulki, babu ko ɗaya da ke tare da Atiku. Dukkan masu ƙarfin siyasa da manyan ’yan siyasa a Adamawa ba sa tare da shi.” In ji shi.

Tinubu ya soki tarihin mulkin Peter Obi

Baya ga Atiku, shugaban ƙasar ya kuma soki tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, kan yadda ya gudanar da mulkin jihar.

Tinubu ya bayyana ayyukan Obi a lokacin da yake gwamna a matsayin marasa wani amfani, inda ya kwatanta irin ayyukan da ya gudanar da cewa ba su kai komai ba.

Kara karanta wannan

Matashin dan APC ya kama sunan Buhari, ya fadi rashin kyautawar da ya yi sa Tinubu a 2023

Tinubu ya yi shagube ga Atiku
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

An ba Tinubu shawara kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiyar siyasa mai suna Ndigbo for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (NDI-ABAT) ta shawarci Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta shawarci shugaban kasar da kada ya mayar da gwamnonin jihohi ginshikin shirin sake zabensa a shekarar 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng