Dalilin Rabuwa da Shi Mu Koma wajen Uba Sani In ji Na kusa da El Rufai

Dalilin Rabuwa da Shi Mu Koma wajen Uba Sani In ji Na kusa da El Rufai

  • Muhammad Bashir Sa’idu, ya zargi Nasir El-Rufai da cin amanarsu duk da sun dade tare a siyasa
  • A yau sun bar jam’iyyar ADC, suka koma APC wajen Gwamna Uba Sani gabanin zaben shekarar 2027
  • Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnan Jihar Kaduna ya ce su ne ke bin Nasir El-Rufai bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Muhammad Bashir Sa’idu wanda yana cikin manyan na-kusa da Nasir El-Rufai ya fadi dalilinsu na barin ADC.

‘Dan siyasar ya zargi Nasir El-Rufai da yaudarar mutanen da suka taimaka masa wajen hawa kujerar gwamna a 2015 da 2019.

Nasir El-Rufai
Tsohon gwamna Nasir El-Rufai lokacin kamfe a Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Bashir Sa'idu ya kare sauya-shekarsu daga ADC

A hirarsa da RFI Hausa aka ji Muhammad Bashir Sa’idu yana sukar tsohon gwamnan na Kaduna, ya jefe shi da cin amanarsu.

Bashir Sa’idu wanda ya yi shugaban ma’aikatan gidan gwamnati ya ce ba su ci amanar mai gidansu da a yanzu yake tsare ba.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru mai takara a jam’iyyar ADC a Kaduna ya tona wa gwamnatin Uba Sani asiri

Bugu da kari, ya ce kafin Malam Nasir El-Rufai ya shiga hannu, sai da shi ya yi zama a gidan gyaran hali na kwana da kwanaki.

Ya ce an shiga sabuwar shekara yana kurkuku har ya kwana 50, bayan ya samu beli kuma sabon alkali ya sake daure shi.

“Ba mu fita mun bari ba sai da muka ga an yaudare mu, an yi mana cin amana a ADC. Kuma muka ga eh da saninsa da yardarsa aka yi mana wannan.
"Sai muka ga dodon da mu ke yi wa tsafi ya nuna mu ba kowa ba ne, ya ma ce ba mu da kowa, bari mu koma inda aka san darajarmu, shi ne muka dawo gidanmu."

- In ji

Doguwar alakar Nasir El-Rufai da Bashir Sa'idu

Alhaji Bashir Sa’idu ya kuma yi tunkaho da sanin El-Rufai, ya ce duk wanda zai yi magana yanzu, daga baya ya san 'Malam'.

Tsohon shugaban na ADC a Arewa maso yamma ya fada wa manema labaran cewa suna tare da El-Rufai tun kafin iyalinsa.

Kara karanta wannan

Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare

Bashir Sa'idu ya ce:

“Duk wanda zai yi maganar banzar nan, ya iske mu ne da malam. Duk a titi ya iske su. Mu’amalarmu ko alakarmu da Malam ya riga har iyalan shi.”

Tsohon kwamishinan ya yi wa El-Rufai gori

Tsohon kwamishinan ya ce su ne wadanda suka roki Malam El-Rufai ya shigo siyasa a APC, amma asalinsa bai san harkar ba.

Ya fada wa gidan rediyon cewa su tun 1992 suke cikin siyasa tsundum, da su aka goyi bayan MKO Abiola a jam’iyyar SDP.

“Wani ya ce maka mu mun zo ne ba a san mu ba a siyasa, albarkacin Nasiru muke ci, wannan karya ne da jahilci.
Muna siyasa Malam Nasiru ya zo ya tarar da mu, ya zo ya tara da mu da turakun mu na siyasa, da turakunmu kuma aka yi amfani.”

- Bashir Sa'idu

Asalin abin da ya kore su daga ADC

Premium Times ta rahoto ‘dan siyasar ya ce bai yi butulci ba kuma shi da irinsu Sulaiman Hunkuyi ne suke bin El-Rufai bashi a siyasa.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa 8 da suka bar APC sun canza shawara bayan haɗuwa da Shugaba Tinubu

Ya dauko yadda suka goyi bayan Jafar Sani Bello ya zama ‘dan takaran ADC, sai aka yi amfani da iyalin El-Rufai aka yi waje da su.

Yake nuna cewa wasu tsirarun bakin mutane aka yi amfani da su wajen ganin Isa Ashiru ya samu takara, a nan suka ce ba za su yi ba.

Isa Ashiru ya caccaki gwamnatin Uba Sani

An samu labari cewa ‘dan takaran ADC a Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya ce Mai girma Uba Sani bai san jihar da yake mulki ba.

Fitaccen ‘dan adawar ya ce Gwamnan Kaduna bai zuwa jiharsa sai bayan makonni biyu, don haka yake ganin bai dace da ofishin ba.

Bayan nan, Hon. Ashiru Kudan ya ce matsalar tsaro tana nan a kwance amma APC ta na yi wa duniya karya da rufa-rufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng