Isa Pantami, Donald Duke da ‘Yan siyasan da Hukuncin Kotun koli Zai Iya Rusa Takararsu
- Kotun ta sake tabbatar da sassan 77(5-7) da 84(2), wadanda suka bukaci mika rajistar ‘yan jam’iyya ga INEC a kan lokaci
- ‘Yan takara kamar Isa Ali Pantami Donald Duke, Kingsley Chinda, da Ovie Omo-Agege na fuskantar barazanar rasa tikiti
- Duk wanda bai cikin sunayen ‘ya ‘yan jam’iyya kafin zaben tsaida gwani ba zai samu damar shiga takara a babban zabe ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A ranar Alhamis da ta gabata, alkalan Kotun koli suka zauna a kan karar da INEC ta shigar kan shafe sashen dokar zabe.

Source: Facebook
Kotun koli ta dawo da sassan dokar zabe
A karshen zaman da aka yi, Kotun koli ta dawo da sassa na 77(5), 77(6), 77(7), da na 84(2) na dokar zabe wanda a baya aka soke su.
Hukuncin da aka yi a karkashin jagorancin Adamu Jauro yana nufin mutum bai isa ya nemi takara a jam’iyyu biyu a lokaci guda ba.
The Cable ta tattaro manyan ‘yan siyasan da ake ganin hukuncin nan zai fi shafa a 2027 domin sun kasance a jam’iyya fiye da daya.
Wadanda takararsu ke cikin barazana a 2027
1. Donald Duke
Tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke shi ne yake yi wa jam’iyyar PRP takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a 2027.
Sai dai ana tsoron babu sunan shi a rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya da sashe na 77 ya bukaci a gabatar kwanaki 30 kafin zaben tsaida gwani.
NAN ba ta dade da rahoto cewa Duke ya shiga PRP daga PDP domin harin zabe mai zuwa ba, sai aka ji ya samu takarar shugaban kasa.
2. Kingsley Chinda
Hon. Kingsley Chinda shi ne yake yi wa jam’iyyar APC takarar gwamna a jihar Rivers a 2027 watanni kadan da sauya-shekarsa daga PDP.
Shi ma hukuncin Kotun koli zai iya taba shi domin sashe na 84(2) ya wajabta zama cikakken ‘dan jam’iyya kafin samun tikitin yin takara.
Sai a watan Yunin 2026 Chinda ya sanar da Majalisar wakilai cewa ya bar PDP kuma ya ajiye mukaminsa, kafin nan APC ta ba shi tuta.
3. Ovie Omo-Agege
Ovie Omo-Agege wanda ya taba zama Mataimakin shugaban Majalisar dattawa a 2023 yana so ya sake zama sanata a shekara mai zuwa.
Inda gizo ke sakar shi ne, sai da ya ga ya rasa tikiti a jam’iyyar APC sai ya yi tsalle zuwa NDC mai adawa kuma aka ba shi takara a Delta.
Leadership ta rahoto shi yana cewa ba a rusa takarar shi ba, amma babu mamaki idan aka yi amfain da sassa na 77 da na 84 ba zai kai labari ba.
4. Victor Ochei
Tsohon shugaban Majalisar dokokin jihar Delta yana neman takarar sanatan Delta ta Arewa a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar NDC.
Kamar dai Omo-Agege, shi ma Victor Ochei sai da kofa ta rufe masa a Mayun 2026 sai ga labari a tashar TVC cewa ya shiga jirgin su Peter Obi.
Bayan kwanaki da sauya-sheka jam’iyyar NDC ta ba Rt. Hon. Ochei damar takarar Majalisar dattawa. A yanzu dai tana kasa, tana dabo.

Kara karanta wannan
Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Source: Facebook
5. Isa Ali Pantami
Isa Ali Pantami shi ma a watan Mayun bana ya rabu da APC zuwa PDP kuma kafin a ce kobo sai aka ji shi ne ‘dan takarar gwamna a Gombe.
Ban da rikicinsa a kotu da asalin ‘yan jam’iyyar PDP, hukuncin Kotun koli zai iya rusa masa takara bisa zargin ya kasance a jam’iyyu biyu.
A zaben tsaida gwani da aka yi a APC, jam’iyyar ta ce Sheikh Pantami ya shiga har ya samu kuri’u 12,120, yana bayan Jamilu Isyaku Gwamna.
Tafiyar Wike tana ganin adawa daga APC
Rahoto ya zo cewa Shugaban APC na reshen jihar Imo ya shawarci Nyesom Wike da ya shiga jam'iyya mai mulki ya daina tsalle-tsalle.
Idan zai fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Bola Tinubu, ana so Ministan na harkokin birnin tarayya Abuja ya rabu da PDP gaba daya.
Austin Onyedebelu ya ce manufar Rainbow Coalition ita ce Wike ya nemi mulkin Najeriya nan gaba a PDP, burin da APC ba za ta yarda da shi ba.
Asali: Legit.ng

