Zaben 2027: Matsayar Kiristoci kan Tikitin Muslim Muslim a Najeriya

Zaben 2027: Matsayar Kiristoci kan Tikitin Muslim Muslim a Najeriya

  • Nentawe Yilwatda ya ce Kiristoci da dama sun amince da tikitin APC na Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima
  • Ya ce babu Kiristan da aka tauye wa haƙƙinsa ko aka muzanta saboda addininsa a cikin shekaru uku na gwamnatin Tinubu
  • Yilwatda ya ambaci kansa, George Akume da Christopher Musa a matsayin Kiristocin Arewa da ke riƙe da manyan muƙamai a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce Kiristoci musamman waɗanda ke Arewacin Najeriya sun gamsu da tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi da jam’iyyar za ta yi amfani da shi a zaɓen 2027.

APC za ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, waɗanda dukkaninsu Musulmi ne, a matsayin ’yan takararta na shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fito da magana kan batun Tinubu bai da lafiyar tsayawa takara a 2027

Nentawe Yilwatda ya yi maganar muslim muslim
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen yakin neman zaben jam'iyyar APC Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today a daren Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026.

Ya ce sabanin yadda lamarin ya kasance a zaɓen 2023, Kiristoci ba su da matsala da tikitin na wannan karon.

APC ta ce Kiristoci na samun kulawa

Shugaban APC ya yi iƙirarin cewa babu wani Kirista da aka muzanta ko aka tauye wa haƙƙinsa saboda kasancewar Shugaba Tinubu Musulmi a cikin shekaru uku na mulkinsa.

Ya ce Kiristoci daga Arewa, ciki har da shi kansa, na riƙe da muhimman muƙamai a gwamnatin tarayya.

Daga cikin waɗanda ya ambata akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya.

Yilwatda ya ce shi kansa Kirista ne kuma shugaban APC na ƙasa, yayin da Akume ma Kirista ne da ke riƙe da muƙamin SGF.

Ya ƙara da cewa akwai ministoci Kiristoci daga Arewa da dama, waɗanda ke jagorantar muhimman ma’aikatun gwamnati.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Wike zai raba biliyoyi don tabbatar da tazarcen Tinubu

Yilwatda ya kare tikitin Musulmi da Musulmi

Shugaban APC ya ce a baya wasu Kiristoci na fargabar cewa tikitin Musulmi da Musulmi zai iya hana su samun wakilci ko murya a harkokin mulki.

Sai dai ya yi iƙirarin cewa wannan fargaba ba ta zama gaskiya ba, saboda a cewarsa, ana jin muryar Kiristoci a gwamnatin yanzu.

Ya kuma bayyana cewa wasu Kiristoci daga Arewa sun samu muƙaman ministoci a ma’aikatun jinƙai da walwala, albarkatun ruwa da tsaro.

Yilwatda ya ce jihar Kaduna ma ta samu Kirista a matsayin ministan gwamnati, lamarin da ya ce bai kasance haka a baya ba.

Ya ce ba a muzgunawa Kiristoci

“Mun tattauna da al’ummomin Kiristoci da dama. Ni kaina Kirista ne, kuma yawancin Kiristocin da muka tattauna da su sun gamsu da tikitin Musulmi da Musulmi.

"Babu wani Kirista da aka muzanta ko aka hana haƙƙinsa da gata saboda shugaban ƙasa Musulmi ne a cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Tinubu.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tsohon abokin takarar Buhari ya bayyana dalilin kin karbar tayin mukamin da Tinubu ya yi masa

Yilwatda ya kuma ce idan ana magana kan haɗa kowa a harkokin mulki, ya kamata a lura cewa Kiristoci na samun muƙamai kuma ana jin muryoyinsu a gwamnatin tarayya.

A ƙarshe, ya yi watsi da ra’ayin cewa tikitin Musulmi da Musulmi zai rage wa APC damar samun ƙuri’u a zaɓen 2027, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.

Nentawe ya ce ba a muzgunawa Kiristoci
Farfesa Nentawe Yilwatda, shugaban jam'iyyar APC na kasa Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Batun lafiyar Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya dage cewa shugaban ƙasar yana da ƙoshin lafiyar da zai iya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaben shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng