A Karshe, ADC Ta Karbi Hukuncin Kotu da Ya Soke Takarar Atiku Abubakar a Zaben 2027

A Karshe, ADC Ta Karbi Hukuncin Kotu da Ya Soke Takarar Atiku Abubakar a Zaben 2027

  • Kwamitin yakin neman zaben ADC ya tabbatar da karɓar sahihin kwafin hukuncin kotu da ya kori shugabancin David Mark
  • Kotun Tarayya ta soke takarar Atiku Abubakar da sauran 'yan takarar da aka zaba a zaben fitar da gwani karkashin jagorancin Mark
  • Jam'iyyar ta zargi gwamnatin APC da kokarin kawo mata cikas, ciki har da rufe Arewa House da aka shirya ganawar Atiku da shugabannin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta jam'iyyar ADC ya tabbatar da cewa ya karɓi sahihin kwafin hukuncin kotu da ya kori shugabancin David Mark.

A makon da ya gabata, wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin tsige Mark daga shugabancin jam'iyyar.

A rahoton Daily Trust, kotun ta kuma soke takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, da sauran 'yan takarar da aka samar karkashin jagorancin Mark.

Kara karanta wannan

Zamfara: An sanar da sakamakon zaben fitar da gwanin dan majalisar tarayyar APC

Alkalin ya yanke hukuncin ne a karar da Nafiu Bala Gombe ya shigar, inda ya kalubalanci yadda Mark ya karbi shugabancin jam'iyyar.

Dan siyasar da ya shigar da karar ya bayyana cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban ADC na shiyyar Arewa, shi ne ya kamata ya gaji shugabancin jam'iyyar bayan tsohon shugaban ya yi murabus.

Sai dai jam'iyyar ADC ta dora alhakin rikicin kan jam'iyyar APC mai mulki, inda ta zargi Shugaba Bola Tinubu da kulla makarkashiyar dakile Atiku ta hanyar amfani da kotuna.

Daga bisani, ADC ta bukaci a ba ta sahihin kwafin hukuncin kotun domin ta shigar da daaka kara.

ADC ta soki lokacin sakin hukuncin

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, daraktan sadarwa da dabarun yada labarai na kwamitin kamfen ADC, Phrank Shaibu, ya ce kotu ta fitar da sahihin kwafin hukunci

Ya ce:

"A karshe, Mai Shari'a Peter Lifu ya fitar da sahihin kwafin hukuncinsa a ranar karshe ta wa'adin kwanaki bakwai da kundin tsarin mulki ya tanada.
"ADC za ta nazarci hukuncin tare da bin dukkan hanyoyin shari'a da doka ta tanada. Sai dai lokacin da aka fitar da shi ya haifar da matukar damuwa, musamman ganin yadda jam'iyyarmu ke ci gaba da fuskantar matakan da ke kawo cikas ga kamfe."

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke kan soke takarar Atiku a 2027, an jero bukatu

Jam'iyyar ADC ta zargi gwamnatin APC

Shaibu ya kuma zargi gwamnatin Jihar Kaduna da rufe Arewa House, wanda aka shirya gudanar da ganawar Atiku da masu ruwa da tsaki daga Arewa a ranar Alhamis.

Ya ce:

"Arewa House wani bangare ne na gadon tarihi da al'adun al'ummomi daban-daban na Arewacin Najeriya. Rufe shi domin hana gudanar da ganawar siyasa cin fuska ne ga al'adunsu da martabarsu.
"Mun gabatar da Arewa House a matsayin wurin da za mu gudanar da ganawarmu da masu ruwa da tsaki ranar Alhamis, amma a yau gwamnatin APC ta yanke shawarar rufe ginin.

Jagororin ADC sun yi fatali da hukuncin kotu

Kun ji cewa kungiyar shugabannin jam'iyyar ADC na Jihohi 19 na Arewa ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta rusa shugabancin jam'iyyar na ƙasa karkashin David Mark.

Shugabannin sun bayyana aniyarsu ta daukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da mika koke gaban Hukumar Shari'a ta Ƙasa (NJC) saboda abin da suka kira sabawa tsarin shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262