Tsohon Gwamna Ya Fito Ya Fadi Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Yake Neman Mulkin Najeriya a 2027
- Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya ce ya shiga takara ne domin magance matsalolin Najeriya tare da inganta rayuwar 'yan kasa
- Duke ya ce Najeriya ta kasa magance matsalar rashin ingantaccen shugabanci tun bayan komawa mulkin dimokuradiyya
- Tsohon gwamnan Cross River ya ce jam'iyyun adawa za su iya kayar da APC idan suka hada kai gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya ce ya fito takara ne domin magance matsalolin da ke addabar Najeriya tare da bai wa 'yan kasar sabuwar damar rayuwa.
Duke ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya nuna damuwarsa cewa Najeriya ta kasa shawo kan matsalar rashin ingantaccen shugabanci tun bayan komawa mulkin dimokuradiyya.

Source: Facebook
Ya yi alkawarin cike gibin shugabancin kasar idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Duke ya soki shugabannin Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Cross River ya ce duk da cewa shugabannin da suka jagoranci Najeriya tun 1979 sun zo da manufofin siyasa, babu wanda ya zo da cikakkiyar manufar shugabanci da za ta samar wa kasar ci gaba da sauyin tattalin arziki.
Duke ya ce:
“An dade ana fuskantar takaici a tsarin siyasar kasar tun bayan komawa mulkin dimokuradiyya. A hakikanin gaskiya, da mun yi fiye da yadda muke a yanzu idan muna da shugabanci nagari.
“An yi gwamnatoci daban-daban, amma babu wacce ta zo da kyakkyawar manufar shugabanci. Wannan ne ya sa na gabatar da kaina domin samar da shugabancin da ake bukata wajen sauya tsarin siyasa tare da samar da ci gaba da kasar ke bukata.
“Mu da ke cikin harkar siyasa ba ma bukatar jifar juna da kalamai, abin da muke bukata shi ne mu gaya wa 'yan Najeriya abin da za mu iya yi domin kasar.”

Kara karanta wannan
Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya sake gamuwa da cikas gabanin zaben 2027
Matsalar da Duke ya hango
Duke ya ce shugabannin Najeriya na baya sun hau mulki ba tare da cikakken tsarin abin da za su yi ba, cewar rahoton Leadership.
A cewarsa, rashin bayyananniyar manufa ta sa gwamnatoci a Najeriya suka ci gaba da kasa biyan bukatun jama'a.

Source: Twitter
Ya kuma ce jam'iyyun adawa za su iya kayar da gwamnatin mai ci idan suka hada kai tare da zaben wanda ya fi cancanta daga cikinsu domin ya jagoranci hadakar adawa.
Dan takarar na PRP ya ce idan jam'iyyun adawa ba su hada kai wajen fuskantar gwamnati mai ci ba, cikin sauki Shugaba Bola Tinubu zai lashe zabe a watan Janairun 2027.
ADC ta hango matsala a hadakar adawa
A wani rahoton, kun ji cewa sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar adawa ta ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan yunkurin hadakar 'yan adawa.
Bolaji Abdullahi ya ce matsayar Peter Obi kan dawo da tallafin mai na iya zama barazana ga shirin haɗa kan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce rashin daidaituwar ra’ayi kan manufofin tallafin mai na iya raunana tubalin da aka kafa sabon shirin haɗin kan jam’iyyun adawa a kai.
Asali: Legit.ng
