Bola Tinubu Ya Sha Mamakin Abin da Jama'a Suka Yi Masa a Jigawa

Bola Tinubu Ya Sha Mamakin Abin da Jama'a Suka Yi Masa a Jigawa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna godiyarsa ga al'ummar jihar Jigawa bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima
  • Shugaban ƙasar ya sha alwashin ƙarfafa gwiwar rundunonin tsaron ƙasar ta hanyar inganta albashinsu da kyautata jin daɗinsu domin shawo kan matsalolin tsaro
  • Tinubu ya ƙaddamar da kayayyakin noma a Jigawa yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kawo nasarori har zuwa shekarar 2031

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna gamsuwarsa matuka tare da miƙa godiyarsa ga jama'ar jihar Jigawa sakamakon gagarumar tarbar da suka yi masa lokacin ziyararsa a birnin Dutse.

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen matsalolin tsaro a ƙasar ta hanyar ci gaba da gudanar da sauye-sauye masu inganci a ɓangaren tsaro.

Kara karanta wannan

Zaben shugaban kasa: ‘Dan Atiku ya zage da yi wa Tinubu kamfe a doke mahaifinsa a Jigawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a wajen kamfen a Dutse. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani sako da ya wallafa a Facebook bayan kammala yakin nema zabe da suka yi a Jigawa.

Tinubu ya yabi Jigawa

A cikin sakon da ya wallafa bayan ziyarar, shugaban ya nuna jin daɗinsa kan yadda mutanen Jigawa suka karɓe shi da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Ya rubuta cewa:

“Jigawa! Na gode sosai! Ina ci gaba da yin murmushi tun daga Dutse. Kun karɓi Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima da ni kamar 'yan uwa, har ma kun sa shugabanku yin rawa! Yau ta kasance rana ta daban. Manomanmu za su samu kuɗi mai yawa a karkashin tsarin mu, matasanmu za su damammaki, sannan iyalai da dama za su ci moriyar ci gaban Najeriya.”

Maganar Tinubu kan tsaro

Haka zalika, lokacin da yake jawabi ga al'umma a filin wasa, Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana ƙarfafa rundunar ƴan sanda da ta sojoji tare da haɓaka albashinsu don ganin an kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce ya gano tarkon da Tinubu ya kafa masa kan bashin da zai ci a waje

“Ina yi muku alƙawari, muna aiki tuƙuru don tabbatar da cewa Najeriya tana da tsaro kuma an kula da dakarunmu da kyau. Za mu ci nasara kan rashin tsaro.
"Mun tsallake yaƙuƙuwa da dama. Za mu kayar da makiyanmu; makiyan haɗin kai, makiyan kwanciyar hankali, da makiyan fatan alheri.”
Motocin tallata Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallan Bola Tinubu a Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi A. Sule
Source: Facebook

Bayan ya ƙaddamar da kayan noma da cibiyoyin koyar da sana'o'i ga matasa, shugaban ya gabatar da tsarin manufofin kamfen ɗin APC mai taken “Daga Sauye-sauye zuwa Nasara,”

Ya mika godiyarsa ga Gwamna Umar Namadi saboda goyon bayansa, yana mai alƙawarin mutunta mutanen Jigawa har zuwa shekarar 2031.

Atiku Abubakar ya Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Tinubu kan shirin karɓar sabon bashin $500m daga Bankin Duniya.

Atiku ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ba shi da ƴancin ɗaura wa gwamnati mai zuwa nauyin sabon bashi a kwanakinsa na ƙarshe a kan karagar mulki.

Ɗan takarar na ADC ya jaddada cewa babu wani shugaban ƙasa da ke shirin barin gado da ke da haƙƙin jefa makomar ƴan Najeriya da ta mai nasara a kansa cikin bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng