‘Maganar Yunwa Fa Ruruta Ta Ake Yi’: Jigon APC Ya Magantu kan Halin Kunci

‘Maganar Yunwa Fa Ruruta Ta Ake Yi’: Jigon APC Ya Magantu kan Halin Kunci

  • Jigon APC kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Alwan Hassan, ya ce ’yan Najeriya ba sa fama da yunwa kamar yadda ’yan adawa ke ikirari
  • Hassan ya ce faduwar farashin wasu kayan abinci a kasuwanni na nuna cewa manufofin gwamnatin Tinubu sun fara haifar da sakamako
  • Ya amince cewa Najeriya ba ta iya samar da isasshen abincin da za ta ci da kanta, yana mai cewa shigo da abinci daga kasashen waje ya zama dole a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Wani jigo a jam’iyyar APC kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Alwan Hassan, ya yi magana kan halin kunci.

Alwan Hassan ya yi ikirarin cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya ba ta kai yadda wasu ’yan siyasa ke kokarin nunawa ba.

Kara karanta wannan

Kakakin yakin neman zaben Tinubu ya ji kunya a idon kowa ana hira a gidan talabijin

Jigon APC ya magantu kan halin kunci
Jigon APC a jihar Kano, Alwan Hassan. Hoto: Alwan Hassan.
Source: Facebook

Hassan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2026.

Jigon APC ya magantu kan halin kunci

Da yake martani kan halin kunci, jigon APC ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewa ’yan adawa ne ke amfani da shi wajen samun tagomashin siyasa.

Ya ce:

“Wannan magana ce ta ’yan adawa. Mutane ba sa cikin tsananin yunwa haka.”

Lokacin da mai gabatar da shirin ya kalubalanci matsayinsa, yana tambayar ko mutanen da ke fama da yunwa za su amince da wannan furuci, Hassan ya ce yana zaune a Najeriya kuma yana sane da halin da ake ciki.

APC ta kare kanta kan halin kunci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

APC ta yi magana kan farashin kayan abinci

Alwan Hassan ya kara da cewa raguwar farashin wasu kayan abinci a kasuwanni na nuna cewa matakan da gwamnatin tarayya ta dauka suna fara yin tasiri.

Ya kuma bayyana cewa manoma na korafin cewa farashin amfanin gonakinsu ya ragu a kasuwanni.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi ya kashe mahaifinsa shugaban APC a yanayi mai tada hankali

A cewarsa, shigo da kayan abinci daga ketare da gwamnati ke yi na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen saukar da farashin kayayyakin abinci.

Sai dai lokacin da aka tambaye shi ko dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje alama ce ta kyakkyawan tafiyar da harkokin noma, Hassan ya amince cewa Najeriya ba ta iya samar da isasshen abincin da zai wadaci al'ummarta a halin yanzu.

Ya ce shigo da kayan abinci wata hanya ce ta wucin gadi da gwamnati ke bi domin cike gibin da ake samu, yayin da ake kokarin bunkasa noman cikin gida.

Hassan ya bayyana cewa:

“Ba za mu iya ciyar da kanmu ba. Amma yayin da muke kokarin cike gibin da ake samu, dole ne mu rika shigo da abinci a halin yanzu.”

Alwan ya fadi nasarorin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Alwan Hassan, ya yi ikirarin cewa lambar gaggawa ta 112 na aiki, ya sa wannan cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu.

Da aka gwada kiran lambar kai tsaye lokacin da ake hira da shi kai-tsaye a gidan talabijin, a karshe sai ‘dan siyasar ya ji kunya.

Malam Alwan Hassan ya nemi a ba gwamnati ƙarin lokaci, yana mai cewa za a kammala daidaita ‘yan matsalolin da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.